in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fa'idar taron JKS da sauran jam'iyyun siyasu na duniya ga ci gaban al'umma
2017-12-29 06:35:21 cri

A kwanakin baya ne, aka rufe taron manyan jami'an Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na jam'iyyun siyasu daban daban na duniya, taron da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin. Manyan kusoshi mahalarta taron sun yi kira ga jam'iyyun siyasu daban daban da su kara amincewa da juna, da musayar ra'ayi, da kokarin hadin gwiwa, don kafa wata sabuwar dangantaka tsakaninsu, da cimma matsaya daya, da girmama juna, da kokarin koyi da juna.

Taron na birnin Beijing shi ne taron manyan jami'ai na farko da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta shirya tare da sauran jam'iyyun siyasa na kasashe daban daban, wanda ya hallara shugabannin jam'iyyun siyasu kimanin 300 na kasashe fiye da 120

Mahalarta taron na ganin cewa, shawarar da babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya gabatar, kamar "samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin duniya", da "shawarar ziri daya da hanya daya" sun shiga cikin zukatan al'umma duniya. Wannan ya sa jami'an suka nuna aniyyar kara yin mu'amala da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kokarin hadin gwiwa da ita a fannoni daban daban.

Kyautata fasahar jam'iyya ta fuskar kula da wata kasa da sauran harkokin siyasa, yana daya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a wajen taron na wannan karo. Inda mahalarta taron suka fi mai da hankali kan irin nasarorin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu a wannan fanni, musamman ma a bangaren ladabtarwa, da yaki da cin hanci da rashawa.

Masu fashin baki na cewa,ya kamata dukkan jam'iyyun siyasun kasashe daban daban su yi koyi da manufar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, saboda tana kokarin dakile cin hanci da rashawa, ta hanyar sauya tunani da kuma daukar matakan magance matsalar daga tushe. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China