in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta kwashi kashinta a hannun Gambiya da ci 2-1 a wasan sada zumunta
2017-11-15 17:43:35 cri
An yiwa Morocco zan kunne data farka daga barci a yayin da ake tunkarar gasar wasannin cin kofin kaasashen Afrika na 2018, bayan da Gambiya ta lallasata da ci 2 da 1.

Morocco ce zata karbi bakuncin gasar wasannin na cin kofin Afrikan daga ranar 12 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Fabrairu, wanda ake saran 'yan wasa daga nahiyar ta Afrika zasu nuna bajintarsu.

A wasan da aka buga a katafaren filin wasa na Marrakech Grand Stadium, Momodou Ceesay yayi nasarar zarawa Gambiya kwallaye biyu bayan fara wasan da mintoci 11 da kuma mintoci 38, yayin da Ahmed Hamoudane ya ciwa Morocco kwallo guda mintoci 45 da fara wasan.

A yunkurinta na neman shiga gasar wasannin cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2018, kungiyar wasan kwallon kafa ta Morocco ta yi galaba akan takwararta ta Mauritania da ci 4-2 a ranar Juma'a.

Amma ga kasar Gambiya, nasarar data samu a wasan share fagen cin kofin kasashen Afrika na 2018, wanda tayi galaba kan Algeria a wasan da suka buga a watan Maris, ya kasance a matsayin wata dama ce ta shirye shiryen shiga gasar ta kasashen Afrika a shekarar 2019.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China