in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kabilar Hani da wakokinsu
2017-08-14 07:15:07 cri
A yankin Honghe mai cin gashin kanta na kabilar Hani da ta Yi da ke lardin Yunnan a kudu maso yammacin kasar Sin, akwai wani kauyen da ake kira Puchun, kuma 'yan kabilar Hani da ke zaune a kauyen tun kaka da kakaninsu su kan rera wakoki a yayin da suke gudanar da aikin gona. Wani lokaci, wani daga cikinsu zai jagoranta, sauran kuma su rika yin amshi bisa Karin sautinsu, wani lokaci kuma, su kan yi waka suna kada kayan kida mai kirtani uku ko kuma su nannada ganyen bishiya suna busawa. Suna yabawa ayyukan gona da soyayya da kuma abubuwan da ubangiji ya hallita a cikin wakokinsu. Sautin wakokin na da armashi, kuma a shekarar 2006, an sanya wannan salon waka a cikin jerin al'adun gargajiya na kasar Sin. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China