in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tasirin maganin gargajiya a harkokin kiwon lafiyan kasashen duniya
2017-07-20 13:56:49 cri

A kwanakin baya ne, aka gudanar da taron ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobin BRICS, kana babban taron ilmin likitanci da maganin gargajiya na kasashen a birnin Tianjin da ke nan kasar Sin.

Kasashen BRICS manyan kasashe ne a fannin ilmin likitanci da maganin gargajiya, ana kuma fatan wannan taron zai bunkasa ilmin likitancin gargajiya, a kokarin amfanawa jama'ar kasashe mambobin BRICS da ma na duniya baki daya. Yanzu haka, ilmin likitanci da maganin gargajiya na kasar Sin ya yadu a kasashe 183.

Gwamnatin kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyi 86 tare da gwamnatocin kasashen waje, da kungiyoyin duniya kan ilmin likitanci da maganin gargajiyar kasar Sin. Yanzu kuma ilmin likitanci da magani na gargajiyar Sin ya zama wani muhimmin bangare na kara mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da kasashe daban daban.

Bayanai na nuna cewa, akwai kasashe fiye da 30 da suka kafa makarantu, da daruruwan kwalejojin koyar da ilmin maganin gargajiyar Sin, da nufin horas da kwararrunsu a wannan fanni. Bugu da kari, a ko wace shekara, akwai dalibai fiye da 13000 da ke zuwa kasar Sin don kara ilminsu a wannan fanni, yayin da mutane fiye da dubu 200 ke zuwa kasar Sin don samun jinya ta hanyar shan maganin gargajiya. Haka kuma, kasar Sin ta tura tawagar ba da jinya zuwa kasashe fiye da 70, a cikinsu, likitoci gargajiyan sun kai kaso 10 cikin dari.

Wata kididdigar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar ya nuna cewa, akwai kasashe 103 da suka amince da hanyar yin allurar gargajiyar kasar Sin, a ciki, 29 sun bullo da dokar amincewa da ilmin likitancin gargajiya, 18 kuma sun shigar da tsarin yin allurar gargajiyar kasar Sin cikin tsarin inshorar kiwon lafiyarsu. Masu sharhi sun bayyana cewa, akwai bukatar masu maganin gargajiya a kasashe daban-daban su gabatar wa masana fasahohin da Allah ya hore musu a wannan fannin don tantancewa, kana gwamnati ta rika karfa musu gwiwa. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China