in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunawa da 'yan wasan da muka yi rashinsu a 2016
2017-01-05 20:49:09 cri

A shekarar 2016, duniyar wasanni ta yi rashin 'yan wasa da dama, da ma jami'ai wadanda suka bada gudummawa ga harkar wasannin.

Wasu daga wadanda za a dade ba a manta da rawar da suka taka a fannin wasanni, da aka yi rashin su a wannan shekara sun hada da fitaccen dan wasan dambe na kasar Amurka Muhammad Ali.

Muhammad Ali dai ya rasu ne a ranar 4 ga watan Yuni yana da shekaru 74 da haihuwa, bayan ya sha fama da cutar makyarkyata tsawon shekaru 32. Ana dai daukar sa a matsayin daya daga 'yan wasan dambe mafiya shahara da suka rayu a karni na 20.

Ali ya lashe kambin dambe ajin masu nauyi har karo 3. Ya kuma yi fice wajen yaki da nuna wariyar launin fata, yayin da a hannu guda yake fama da cutar makyarkyata tsawon lokaci.

A shekarar 1960, Ali ya lashe kambin damben ajin masu nauyin kilogram 81, amma ya jefa lambar da ya samu cikin kogin birnin Ohio, domin nuna rashin amincewar sa ga irin wariyar da ake nunawa bakaken fata a Amurka.

An nada Ali jakadan zaman lafiya na MDD a shekarar 1998. Ya kuma sadaukar da rayuwar sa wajen yaki da nuna wariya da tabbatar da adalci, baya ga burin sa na ganin bil adama ya rayu cikin daidaito.

1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China