in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hajiya Asma'u Ahmed Makarfi
2015-05-12 16:39:04 cri

Yau shirin In Ba Ku Ba Gida yana farin cikin gayyato wata bakuwa mai suna Hajiya Asma'u Ahmed Makarfi, wata jaruma a fagen yaki da barace barace a arewacin Najeriya ta hanyar shirin Millenium Hope Progamme.

Millenium Hope Programme wani shiri ne na musamman da Hajiya Asma'u ta kirkiro domin taimaka ma yara almajirai wajen samun ingantaccen rayuwa kamar sauran 'yan uwansu masu galihu. Wannan shiri da aka bullo da shi yau fiye da shekaru goma yana nan a jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya, kamar yadda Hajiya Asma'u ke fata, yana nan yana inganta rayuwar wadannan bayin Allah da suka tsinci kansu a cikin wannan hali na barace barace, abin da ya kasance ba laifinsu ba ne sai ma dai a ce kaddarar rayuwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China