Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2018-07-02 10:26:28    
Harin bam ya hallaka mutane 15 tare da jikkata wasu da dama a gabashin Jalalabad

cri
Kimanin mutane 15 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 20 suka jikkata, sakamakon fashewa da ta tsarwatsa wata mota a gabashin birnin Jalalabad dake lardin Nangarhar na gabashin Afghanistan.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin gwamnatin kasar Attaullah Khogiani, ya ce fashewar ta shafi kasuwar Mukhabirat, inda nan take ta hallaka mutane 15, galibinsu fararen hula.

Rahotanni sun ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti, kana jami'an tsaron kasar sun fara aiwatar da bincike kan lamarin. Kawo yanzu dai babu wani mutum, ko wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin.

Harin dai na ranar Lahadi, ya auku ne a lokacin da shugaban kasar Mohammad Ashraf ke halartar wani taron jami'ai, da wasu jagororin lardin. An ce an kira taron ne domin tattaunawa game da yadda za a bunkasa yunkurin gwamnatin kasar na wanzar da zaman lafiya, tare da karfafa gwiwar mayakan Taliban su rungumi tattaunawa da tsagin gwamnati, ko a kai ga kawo karshen tashe tashen hankula dake addabar kasar. (Saminu Hassan)