Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-02-08 11:01:39    
An yi makon al'adun kasar Sin a unguwoyin kasar Masar

cri
A ranar 5 ga wannan wata a yayin kusantowar ranar bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin, wato bikin shekarar damisa da ke alamanta shekarun haihuwa na mutanen kasar Sin bisa kalandar gargajiya , cibiyar al'adun kasar Sin da ke birnin Alkahira ta shirya bikin murnar yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin na shekarar 2010 , wato makon al'adun kasar Sin a birnin Alkahira na kasar Masar.

Jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Masar Wu Chunhua da 'yan diplomasiya na kasashe daban daban da ke wakilci a kasar Masar sun halarci bikin bude makon al'adun kasar Sin, kuma jama'ar da suka zo daga rukunoni daban daban na kasar Masar da Sinawan da ke zama a kasar Masar sun halarci bikin da duk sauran shagulgulan da aka shirya a wannan rana. A gun bikin, Jakadan kasar Sin Wu Chunhua ya yi jawabin fatan alheri cewa, a albarkacin kara zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da kara yin ma'amala da kasashen waje a kowace rana, bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin ya kara jawo hankalin mutanen duniya, ta hakan, an bude wa duk duniya wata tagar kara fahimtar al'adun kasar Sin. Mun shirya aikace-aikacen murnar bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin a birnin Alkahira musamman domin yin gado da yadada nagari na kowa mai kyau na gargajiya na kaunar zaman rayuwa da ba da hasashen bin da'a da nuna kauna ga jama'a da kafa unguwoyin al'adu da ke kasancewa cikin zaman lafiya da jituwa da kara sanin al'adun kasashen duniya ta hanyar wannan bikin gargajiya, duk domin mayar da duk duniya cikin kauna da alheri da zaman lafiya da samun bunkasuwa.

A cibiyar al'adun kasar Sin da ke birnin Alkahira , an yi ta shirya irin bukukuwa a jerin shekaru da dama, wannan ya sami maraba da karbuwa da kauna daga rukunoni daban daban na kasar Masar, a shekarar da muke ciki, cibiyar tana fatan za a kara bayyana wa mutanen kasar Masar al'adun gargajiya na kasar Sin ta hanyar shirya aikace-aikacen murnar bikin yanayin bazara don yadada al'adun kasar Sin , wata mai ba da shawara ga jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Masar madam Chen Dongyun ta bayyana cewa, aikace-aikacen da muka shirya a wannan shekara don murnar bikin yanayin bazara na kasar Sin sun karya matsayin da aka yi a da. A da, mun kan shirya bukukuwa a cibiyarmu kawai, amma a shekarar da muke ciki, mun yi hadin gwiwa da wasu club da hukumomi da unguwoyi don yadada abubuwan da ke da nasaba da bikin yanayin bazara zuwa duk duniya, muna fatan za mu yi bikin bisa matsayin wata lambar al'adu mai kyau a yayin da muke murnar bikin tare da mutanen duk duniya .

A shekarar da muke ciki, za mu shirya makon al'adun kasar Sin don murnar yanayin bazara na gargajiya a filin mazauna birnin Rehab na kasar Masar, ban da kallon wasanni, sai mutanen birnin za su iya dandana abinci iri iri na gargajiya na kasar Sin. Bayan da tsohon jakadan kasar Masar da ke wakilci a kasar Sin Mahmoud Allam ya kammala kallon wasannin da aka yi , sai ya bayyana cewa, na zo nan don murnar bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin, inda na tuna da abubuwa masu kyau da yawa da na ji na gani a kasar Sin. Game da al'adar gargjiya ta kasar Sin ta nuna wasan wuta, ana iya cewa, dare da rana tamkar dukkansu daya ne suke yi , sai haske a ko'ina ake ciki ba tare da duhu ba. Mr Mahmoud ya kuma nuna yabo ga makon al'adun kasar Sin da aka shirya a unguwoyin birnin Alkahira.(Halima)