Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-02-01 13:38:11    
An rufe taron shekara shekara na Daovs

cri

A ranar 31 ga wannan watan jiya a birnin Daovs na kasar Switzeland, an kawo karshen taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan batun tattalin arzikin duniya wanda aka yi kwanaki biyar ana yinsa. Masana da kwararru na rukunonin siyasa da na fasahohi da na kasuwanci da yawansu ya wuce 2500 sun halarci tarurukan tattaunawa kan batutuwan musamman fiye da 200, inda suka yi tattaunawa sosai kan karuwar tattalin arzikin duniya da yin kwaskwarima kan tsarin harkokin kudi da sarari da kalubale wanda sauyawar yanayi ya kawo da kuma sake raya kasar Haiti da yadda za a aiwatar da ayyukan shimfida da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da halin da ake ciki a kasar Afgannistan da sauran manyan batutuwa, don neman samun amsa ga tambayar da aka yi dangane da wane irin hanyar da za a bi don bunkasa tattalin arzikin duniya bayan abkuwar rikicin kudi da neman sabon tsarin yi wa duk duniya kwaskwarima.

Daya daga cikin manyan batutuwan da suka jawo hankalin mutane a gun taron shi ne , yadda za a yanke shawara kan halin da ake ciki yanzu na bunkasa tattalin arzikin duniya. Ko tattalin arzikin duniya ya riga ya kama hanyarsa ta farfadowa? Ko tattalin arzikin yankin da ake yin amfani da kudin Euro ya iya dagulewa sosai sakamakon rikicin bashin da kasar Switzeland ta ci? Game da wadannan batutuwa, bangarori daban daban suna da ra'ayoyinsu daban daban. A cikin jawabinsa, mataimakin firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke halartar taron Daovs ya bayyana cewa, rikicin kudi na kasa da kasa bai sauya halin da kasar Sin take ciki na raya tattalin arziki da samun makoma mai kyau ba, kasar Sin tana da karfin daidaita rikitacen halin da ake ciki da kuma ci gaba da raya tattalin arzikinta yadda ya kamata, ya bayyana cewa, kamata ya yi tattalin arzikin duniya na nan gaba zai bi hanyar samun bunkasuwa bisa daidaici a dogon lokaci, kuma gamayyar kasa da kasa za su kara daidaita manufofinsu a dukkan fannoni da yin hadin gwiwa a tsakaninsu ta yadda tattalin arzikin duniya zai sami farfadowa a dukkan fannoni, kuma dole ne kasuwannin duniya za su kara bude kofofinsu , kuma za a raya duk duniya bisa daidaici.

Wami mai ba da shawara ga shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa, kasar Amurka da kasashen Turai da sauran kasashe yanzu ba su da karfi sosai ga farfado da tattalin arziki, kodayake sun riga sun sami karuwar tattalin arziki, amma wadanda suka rasa aikin yi sai kara yawa suke yi. Babban shugaban asusun kudin kasashen duniya ya kuma bayyana cewa, a sa'a da gwamnatocin kasashe daban daban suke watsi da matakan sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, ya kamata su yi ayyuka cikin tsanake, kada a mayar da tattalin arziki mai farfadowa ya sake dagulewa sosai.

Yadda za a kara sa ido kan harkokin hukumomin kudi ya zama batu mafi muhimmanci da aka yi tattaunawa a kai a gun taron. Rikicin kudi na duk duniya da ya faru sakamakon rikicin rancen kudi da aka bayar wa mutane marasa lamuni mai karfi a kasar Amurka ya sa mutane suka gani mugun sakamakon da aka kawo sakamakon rashin sa ido kan harkokin kudi da rashin sarrafa aikace-aikacen neman ribar kudi ba bisa doka ba. Shi ya sa shugabannin kasashen Amurka da Turai da suka fama da rikicin sun yi lashin takobi cewa, za su yi kwaskwarima sosai kan tsarin kudi.A makon jiya, shugaban kasar Amurka Obama ya gabatar da wani sabon mataki na kara karfi ga kula da manyan mutanen rukunonin kudi na "Wall Street" don yi wa manyan bankunan kasar Amurka tabaibayen shiga aikace-aikacen neman ribar kudi ba bisa doka ba.

Shugaban kasar Korea ta Kudu da shugaban kasar Mexico su ma sun halarci taron. Lee Myung Bak , shugaban kasar Korea ta Kudu yana ganin cewa, ya kamata shugabannin da ke halartar taron su bayyana matsayinsu na nuna adawa da ra'ayin yin kariya kan cinikayya da zuba jari. Shugaban kasar Mexico Feipe Calderon ya kirayi kasashe daban daban da su yi maganin sauyawar yanayi tun da wurwuri.(Halima)