Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 16:59:39    
Yawan GDP da Sin za ta samu a masana'antar yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli zai kai yuan biliyan 2800 a shekarar 2012

cri
Ran 8 ga wata, a nan Beijing, Xie Zhenhua, mataimakin shugaban kwamitin ofishin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya bayyana cewa, an kiyasta cewa, a shekarar 2012, yawan GDP da kasar Sin za ta samu a masana'antar yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli zai kai kudin RMB Yuan biliyan 2800.

A wannan rana, an yi taron dandalin tattaunawa kan yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli a tsakanin Sin da Japan a karo na 4. A yayin taron, Xie Zhenhua ya yi bayani da cewa, muhimman fannoni da manyan ayyukan da kasar Sin ke mai da hankali a kai ta fuskar raya masana'antar yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli su ne rubanya kokarin raya masana'antar yin tsimin makamashi, da inganta karfin masana'antar bola-jari, da habaka masana'antar kiyaye muhalli, da kyautata fasahohi da injuna, da yayata yin amfani da kayayyakin yin tsimin makamashi, da gaggauta bunkasa masana'antar ba da hidimomi ta fuskar yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli.(Tasallah)