Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 18:24:18    
Za a karfafa hulda tsakanin Sin da kasashen Afrika??Kai ziyara ga babban malami na sashen kula da dangantaka tsakanin kasa da kasa, da harkokin diplomasiya na jami'ar Nairobi

cri

Za a shirya taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika nan gaba ba da dadewa ba a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar. A yayin taron, za a yi kokarin kimanta yanayin da ake ciki na tabbatar da ayyuka da za a yi nan gaba na taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar a dukkan fannoni, kana za a tsara wani shiri game da hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika a shekaru uku masu zuwa. To, wane irin tasiri ne bunkasuwar kasar Sin za ta kawo ga Afrika? Kuma mene ne ra'ayoyin bangarori daban daban na kasashen Afrika game da dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afrika a yanzu? Wane irin fata ne suke nunawa ga wannan taron ministoci? Kwanan baya, wakilanmu sun kai ziyara ga babban malami na sashen kula da dangantaka tsakanin kasa da kasa, da huldar diplomasiya na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya Garrishon Ikiara. To, yanzu ga cikakken bayanin.

Mr. Garrishon ya taba zama sakataren ma'aikatar zirga-zirga na kasar Kenya. A yayin da yake kan kujerar, ya taba kawo ziyara ga kasar Sin har sau biyu. Ya ce, kasar Sin na samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, karfinta na samun karuwa, kazalika kuma tana ta kara yin mu'ammala tare da kasashen Afrika a fannoni daban daban. 'A ganina, kasar Sin na kara taka muhimmiyar rawa a kasashen Afrika, musamman ma a fannin tattalin arziki. Kasar Sin wata muhimmiyar aminiya ce ta kasashen Afrika. Kasar Sin kuma ta bayar da taimako sosai ga kasashen Afrika a fannonin manyan ayyuka, da aikin ba da ilmi, da al'adu, da kuma ba da hidimar zaman takewar al'umma. Muna fatan ta wannan taron ministoci na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin bangarorin biyu, za mu kara hada kai a fannoni daban daban, musamman ma a fannonin kimiyya da fassaha, da aikin ba da ilmi, da dai sauransu, domin raya dangantakar hadin kai irin ta nuna moriya ga juna tsakanin Sin da kasashen Afrika.'
1 2 3