Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 22:16:12    
Sin na fatan ci gaba da karfafa dangantakar sada zumunci da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika daga dukkan fannoni

cri

A ranar 4 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Afrika, a karkashin inuwar "cimma moriya cikin daidaito da samun hakikanin da samun bunkasuwa daga dukkan fannoni, domin yin amfani da wannan dama domin fuskantar kalubaloli tare da ci gaba da daukar hakikanin matakai domin kara ingiza dangantakar hadin gwiwa da sada zumunci daga dukkan fannoni.


Ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta bayyana cewa, tattalin arzikin Sin da na kasashen Afrika na dogara da juna sosai, kuma akwai makoma mai haske wajen yin hadin gwiwa tsakaninsu, a shekarun nan da ake ciki, a karkashin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta yi ta samun bunkasuwa, kuma mu'amalar tattalin arziki tsakaninsu na samun karfafuwa, kana hadin gwiwa tsakaninsu ya kara samun ci gaba, kasashen Afrika sun riga sun zama manyan abokan kasar Sin wajen aikin hadin gwiwa.


Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu, kasar Sin na da alakar ciniki da kasashen Afrika 53. Jimillar kudaden cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta zarce dalar Amurka biliyan 10 daga shekarar 2000, kuma ta kan karu da kashi 33 cikin kashi 100 a ko wace shekara, a yayin da, a shekarar bara, jimillar kudin cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta zarce dalar Amurka biliyan 100.


Kana, bisa kididdigar da ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta bayar, an ce, tare da samun bunkasuwar tattalin arzikin Sin da kyautatuwar yanayin zuba jari a kasashen Afrika, sha'anin saka jari da kasar Sin take samu a kasashen Afrika na samun bunkasuwa sosai.


Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun bayan da aka yi taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika na shekarar 2006, Sin ta dauki matakai wajen kafa asusun ba da lamuni na samun bunkasuwar kasar Sin da kasashen Afrika, da gina yankunan hadin gwiwa a sha'anin cinikayya a kasashen waje, da nuna goyon baya da sa kaimi ga masana'antun Sin da suka zuba jari a kasashen Afrika. Kuma sha'anin saka jari da kasar Sin ta kan gudanar a kasashen Afrika na samun bunkasuwa sosai.


Yayin da kasar Sin ke zuba jari ga kasashen Afrika, ta samar musu da  fasahohi, kuma Sin ta kara yawan kudaden haraji da aikin samar da guraben aikin yi a wurin da horar da kwararru da nuna goyon baya ga samun bunkasuwar tattalin arziki a kasashen Afrika.


Kazalika, a wannan rana, ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta ce, gudummawar da kasar Sin ke samarwa kasashen Afrika ba ta kawo lahani ga moriyar ko wace kasa ba.


A cikin shekaru 50 da suka wuce, Sin ta nace ga aikin ba da gudummawa ga kasashen Afrika bisa gwargwadon karfinta. Sin ta ba da gudummawa ga kasashen Afrika bisa hanyar girmamawar kasashen Afrika da taimaka musu wajen samun bunakasuwar tattalin arziki kuma ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba, kana Sin ba ta kutsa kai kan harkokin siyasa na kasashen Afrika ba, a sakamakon haka, Sin ba ta kawo lahani ga moriyar ko wace kasa ba.


Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta Sin ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta gina manyan ayyuka sama da 900 ga kasashen Afrika sama da 50, kuma sun hada da sha'anin kiwon dabbobi da samar da amfanin ruwa da wutar lantarki da sadarwa da sufuri da abinci. Haka kuma Sin ta soke basussukan da kasashen Afrika masu talauci 33 da suka ci daga gare ta. Kuma tun daga shekarar 1963 watau Sin ta tura ayarin aikin jinya na farko ga kasashen Afrika, ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta tura mambobin ayarorin aikin jinya ga kasashen Afrika sama da dubu 17.(Bako)