Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 22:03:31    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi bayanin fatan alheri ga sabuwar mujallar Sin da Afirka

cri

Bisa wani labarin da jaridar labaru da babi na kasar Sin da aka buga a ran 2 ga wata ta bayar, an ce, a kwanan baya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi bayanin fatan alheri ga sabuwar mujallar Sin da Afirka wadda mujalla ce game da taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.

A cikin bayanin da Hu Jintao ya yi, an ce, jama'ar kasar Sin suna mai da hankali a kan zumuncin al'ada a tsakaninsu da jama'ar Afirka, kuma a ganinsu jama'ar Afirka abokai ne na arziki, don haka suna son zama abokan jama'ar Afirka har abada. Ban da haka kuma, yana fatan mujallar Sin da Afirka ta ba da gudumawa ga kara dankon zumanci da sa kaimi ga kara yin mu'amala da kara yin hadin gwiwa da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Afirka.An kafa mujallar Sin da Afirka a shekarar 1988, kuma ana buga wannan mujallar ne da harshen Faransanci da Turanci, ita ce jarida daya da kasar Sin take buga wa masu karatu daga Afirka.(Abubakar)