Har wa yau kuma, Mista Meng ya nuna cewa, Sin da Amurka, muhimman kasashe biyu ne a duniya, wadanda ke da babban nauyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Shi ya sa kamata ya yi Sin da Amurka su kawar da bambancinsu, da kara samun fahimtar juna, a kokarin raya sabuwar dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.
Shugaban hukumar kula da harkokin waje ta ma'aikatar tsaron kasar Sin Manjo Janar Qian Lihua ya bayyana cewa: "An samu sakamako mai kyau a yayin ziyara a wannan gami. Muna da imanin cewa, muddin bangarorin biyu suka yi kokari cikin hadin-gwiwa, dangantakar rundunonin sojan kasashen biyu zata bunkasa yadda ya kamata."(Murtala) 1 2 3
|