Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-28 09:16:58    
'Dan wasan kwallon kafa daga kasar Brazil Ailton yana yin wasa a kasar Sin

cri

A tsakiyar watan Yuli na bana, wani sabon 'dan wasa tauraro ya shiga babbar hadaddiyar gasar kwallon kafa ta kasar Sin, wannan 'dan wasa shi ne Ailton Goncalves Da Silva wanda ya zo daga kasar Brazil. Bana, Ailton yana da shekaru 36 da haihuwa, ana kiransa da suna "walkiya mai siffar kwallo", dalilin da ya sa haka shi ne domin tsayinsa bai wuce mita 1.74 ba, kuma yana da kiba kadan, a sanadin haka, siffar jikinsa ta yi kama da kwallo, amma ya kan yi gudu da saurin gaske, har yana iya gudun mita dari daya cikin dakika 10.5, shi ya sa ake kiransa da wannan suna. Ailton ya taba buga wasa a kungiyar Bremen ta kasar Jamus, ya ce,  "Da, na taba buga wasa a kasar Jamus, a wancan lokaci, na fi duk daukacin 'yan wasan kwallon kafa na kasar Jamus sauri saboda na kan yi karawa da doki, amma yanzu kila ba haka ba ne. Duk da haka, saurin gudu ba abu ne mafi muhimmanci ga 'dan wasan kwallon kafa ba. Ina ganin cewa, hadin gwiwa tsakanin abokan wasa ya fi muhimmanci."

Lallai Ailton ya fi son yin gasar gudu da doki. A kasar Brazil, Ailton yana da wani gidan noma mai fadi, yana kiwon dawaki da yawa a ciki. In ya samu lokaci, ya kan yi gasar gudu da su. Ban da wannan kuma, Ailton ya fi son gasar kaboyi, wato 'cowboy' a turanci. Tun lokacin da yake yaro karami, ya yi mafarki biyu, dayan kuma cikinsu shi ne yana fatan zai zama wani 'dan wasan kwallon kafa, wani daban shi ne yana fatan zai zama wani kaboyi. Daga baya, Ailton ya yi zaben zaman wani 'dan wasan kwallon kafa na sana'a musamman ma domin neman samun kudi. Duk da haka, sha'awarsa kan gasar kaboyi ba ta ragu ba ko kadan. Ailton ya ce,  "Idan na samu lokaci, sai na je kallon gasar kaboyi, kuma na kan shiga gasa. Na ji an ce, fasahata ta hawa doki ta fi ta wasan kwallon kafa. Koda yake na kan ji ciwo a yayin gasar kaboyi, amma har yanzu ina kaunarta."

A shekarar gasa tsakanin shekarar 2003 da ta 2004, Ailton ya taba buga wasa a kungiyar Bremen ta kasar Jamus, a wannan shekara, ya jefa kwallaye 28 cikin raga, har an zabe shi da ya zama fitaccen 'dan wasan kwallon kafa na kasar Jamus wanda shi ne fitaccen 'dan wasa na farko da ba 'dan asalin kasar Jamus ba a tarihi. Amma, Ailton bai samu damar shiga kungiyar kwallon kafa ta kasar Jamus ba, ya yi bakin ciki sosai, amma yanzu ya kasa kula da wannan. Ya ce,  "A kasar Brazil, ba dukkan 'yan wasan kwallon kafa ke iya samun biyayyan da ake nuna musu ba, shi ya sa na je kasashen Turai domin buga wasa. Yanzu ina buga wasa a kasar Sin, ina kaunar kasar Sin sosai. Zan yi iyakacin kokari domin bauta wa kungiyar Chongqing ta kasar Sin. Amma iyalina suna kasar Brazil. A kasar Brazil, fitattun 'yan wasan kwallon kafa suna da yawa, ba zai yiwu ba kowane 'dan wasa ya shiga kungiyar kasa, a sanadin haka, 'yan wasan kasar Brazil da yawa su kan je kasashen Turai ko kasashen Asiya domin buga wasa."

A shekarar 2004, hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Qatar ta yi kokarin shigar da 'yan wasan kasar Brazil uku da suka hade da Ailton cikin kasarta domin neman samun damar shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006, wato a madadin kasar Qatar, wadannan 'yan wasa uku za su shiga gasa ta mataki na farko a shiyyar Asiya bisa matsayinsu na 'yan asalin kasar Qatar. Amma a karshe dai, kasar Qatar ba ta cim ma burinta ba saboda an hana ta yin haka. Duk da haka, idan an sake gayyatar shi da ya shiga wata kasa daban domin buga wasa, Ailton zai yi la'akari kan wannan.

Ailton ya taba yin wasa a kungiyoyi daban daban na kasashe daban daban, alal misali, kasar Jamus da kasar Turkiyya da kasar Serbia da kasar Austria da kuma kasar Brazil, game da wannan, Ailton ya bayyana cewa,  "A cikin 'yan shekarun da suka shige, ban samu zama daram ba, koda yaushe na kan kaura daga wani na wuri zuwa wani daban, amma na ji dadin irin wannan hali, kasar Sin da kasar Turkiyya da kasar Jamus da kasar Brazil da sauransu. Duk wadannan wurare sun yi bamban da juna sosai, wajen al'adu ko hanyoyin zaman rayuwa, ina kaunar abubuwan da suka yi bamban, wato abubuwa ba su tashi daidai da juna ba."

A watan Yuli na bana wato shekarar 2009, Ailton ya tsai da cewa, zai zo kasar Sin domin buga wasa. Koda yake ya riga ya kai shekaru 36 da haihuwa, amma saurin gudu da fasahar wasa da Ailton yake da su sun kai matsayin koli a duniya. A cikin mintoci 40 kawai, Ailton ya ci jarrabawar da kungiyar Chongqing ta kasar Sin ta yi masa, daga baya kuma sun kulla wata kwangila mai tsawon watanni shida, ya samu albashin da yawansa ya kai dalar Amurka dubu dari uku da hamsin. Amma Ailton bai ba da gudummawa ga kungiyar Chongqing kamar yadda aka kimmanta ba. Kan wannan batu, Ailton ya dauka cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin bai samu goyon baya daga wajen abokan wasansa ba tukuna. Ya ce,  "Yayin da nake gudu a gaba, sauran 'yan wasa ba su mika mini kwallo, shi ya sa na kan yi aikin banza, abin bakin ciki shi ne kokarina ya bi ruwa. Ina tsammani cewa, hadin gwiwa tsakanin abokan wasa ya fi muhimmanci. Yanzu kungiyar Chongqing tana cikin mawuyacin hali, akwai wuya sosai dake gabanmu, ba wanda ya san me zai faru. Amma ba za mu daina yin kokari ba."

Birnin Chongqing yana kudu maso yammacin kasar Sin, kuma yana bakin kogin Yangtse, wato tsakanin mafarin kogin da tsakiyar kogin. An gina birnin Chongqing ne a kusa da duwatsu, shi ya sa ake kiransa da suna "birnin dutse", hanyoyin wannan birni ba a fili suke ba, a sanadin haka, Ailton bai fara tuka mota a wurin ba tukuna koda yake a ko da yaushe yana kaunar sauri da kuzari. Duk da haka, Ailton yana jin dadin zaman rayuwa mai sauki a birnin Chongqing. Ya ce,  "Ina son in tuka mota a birnin Chongqing, amma akwai cunkuson motoci sosai a nan, kuma ban fahimci hanyoyin kan dutse ba tukuna, shi ya sa ban iya tuka mota ba a nan. Na kan shiga tasi idan na fita waje, direbobin tasi na birnin Chongqing suna iya tuka mota sosai. Ina jin dadin zaman rayuwa a nan, kuma na riga na saba da irin wannan hanyar zaman rayuwa, ni daya ne kadai a nan kasar Sin, na kan je dakin atisaye, da wurin gasa, da na cin abinci, na kan je kallon sinima, kuma na yi barci a gida, to, shi ke nan, wannan shi ne zaman rayuwata a kasar Sin." (Jamila Zhou)