Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-21 14:38:56    
Za a yi zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a kasar Afghanisan

cri

A ran 20 ga watan nan hukumar zabe mai zama kanta ta kasar Afghanistan ta sanar da cewa za a yi zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a ran 7 ga watan Nuwanba a kasar saboda daga cikin 'yan takara babu wanda ya samu rabin kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka yi ran 20 ga watan Augusta, saboda haka 'yan takara biyu wato su shugaban kasa mai ci Hamid Karzai da tsohon ministan harkokin waje Abdullah Abdullah da suka fi samun yawan kuri'u za su shiga takara a zagaye na biyu. Bisa sabon sakamakon zabe da hukumar zabe mai zama kanta ta Afghanistan ta bayar, an ce Hamid Karzai ya samu kashi 49.67 bisa dari na kuri'un da aka kada a zaben zagaye na farko. Kafin wannan an labarta cewa Abdullah Abdullah ya samu kashi 30 bisa dari na kuri'un da aka kada. Bisa dokokin zabe na Afghanistan, idan babu dan takara da ya samu rabin kuri'u,za a yi zabe a karo na biyu cikin makonni biyu bayan da aka sake kidaya yawan kuri'un da aka kada,a bar 'yan takara biyu da suka fi samun yawan kuri'un su shiga takara.

A wannan rana Hamid Karzai da John Kerry,shugaban kwamitin harkokin waja na majalisar dattijai na Amurka wanda ya je kasar Afghanistan domin kai ziyara da Kai Eide,wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Afghanistan sun halarci taron manema labaran da aka shirya a fadar shugaban kasa inda Karzai ya amince da kudurin da hukumar zabe ta bayar. Karzai ya ce labaran magudi da aka baza sun kawo shakku kan halalcin zaben shugaban kasa a zagaye na farko,shawarar da hukumar zabe ta tsayar ta dace da tsarin mulkin kasa da dokoki na kasar Afghanistan,wannan zai sa kaimi ga ci gaban yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Afghanistan. Mr John Kerry ya yaba da Karzai kan amincewarsa da a yi zabe na zagaye na biyu. Ya ce wannan matakin da aka dauka ya kawo muhimmin juyi a halin kaka-nika-yi da Afghanistan ta sami kanta a ciki a wasu makonni.

1 2 3