Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-08 19:50:34    
Ana ci gaba da fama da halin rashin tabbas a kasar Madagascar

cri

A ran 6 ga wata da dare a birnin Antananarivo, manyan jam'iyyun siyasa hudu na Madagascar sun cimma daidaito a kan raba muhimman mukamai na gwamnatin wucin gadi ta kasar, abin kuma da ya share fagen samun sulhu a kasar. Amma duk da haka, ana ci gaba da shakkar ko bangarori daban daban na kasar za su iya tabbatar da daidaiton da suka cimma.

A watan Disamba na shekarar da ta gabata, shugaban kasar na lokacin, Marc Ravalomanana ya ba da umurnin rufe gidan rediyo da na telebijin mallakar Andry Rajoelina, wato magajin garin birnin Antananarivo, abin kuma da ya yi sanadiyyar barkewar tashe-tashen hankali da rikicin siyasa a kasar. A ran 17 ga watan Maris na wannan shekara, an tilasta wa Marc Ravalomanana yin murabus daga mukaminsa, abin da ya sa shi fara zaman gudun hijira a kasashen waje.

Domin neman daidaita rikicin siyasa da ake fama da shi a Madagascar, a ran 6 ga wata, wakilan MDD da na tarayyar Afirka da na kungiyar raya kudancin Afirka da na kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci sun yi shawarwari da manyan jam'iyyun siyasa hudu na Madagascar, inda wakilan jam'iyyun suka cimma daidaito a kan yadda za a raba muhimman makaman da ke cikin hukumar wucin gadi, wato shugaba mai ci yanzu Andry Rajoelina zai ci gaba da zama shugaban hukumar wucin gadi, a yayin da Emmanuel Rakotovahiny, wanda ke goyon bayan tsohon shugaba Albert Zafy zai zama mataimakin shugaban hukumar. Sa'an nan kuma, wani magoyin bayan tsohon shugaba Didier Ratsiraka, wato Eugene Mangalaza zai zama firaministan wucin gadi.

1 2 3