Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-02 19:09:20    
Kasashen duniya sun nuna babban yabo ga shagalin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin da jawabin Hu

cri
Ran 1 ga wata, a filin Tian'anmen da ke nan Beijing, an yi babban taron murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Kasaitaccen shagali da kuma muhimmin jawabin da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi sun jawo hankalin kasashen duniya sosai.

A kasar Japan, jaridun Asahi Shimbun da Yomiuri Shimbun da sauran muhimman kafofin yada labaru sun watsa labaru kan bikin duba faretin soja da kuma jawabin shugaba Hu nan take ba tare da bata lokaci ba.

Sa'an nan kuma, Masashi Nonaka, mamban tawagar birnin Tokyo ta Japan wadda ke neman samun damar shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2016 ya kalli bikin duba faretin soja na kasar Sin ta gidan talibijin a lokacin da yake halartartaron kwamitin wasannin Olympic na duniya a birnin Copenhagen na kasar Denmark a ran 1 ga wata. Ya gaya wa wakilinmu cewa,"Na taba yin aiki a Beijing daga shekarar 2004 zuwa ta 2008. Yau na kalli bikin faretin soja na kasar Sin a otel. Wannan harka ce mai ban sha'awa. Ina taya jama'ar Sin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar."

Ban da wannan kuma, a ran 1 ga wata, manyan kafofin yada labaru na kasar Amurka su ma sun ba da labaru filla-filla a kan bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin.

A cikin labarin da ta bayar, jaridar Washington Post ta ce, a yayin bikin duba faretin soja, a karo na farko kasar Sin ta nuna sabbin makamai masu nau'o'i da dama da ta nazarta da kuma kera su da kanta, ta nuna nasarorin da ta samu ta fuskar raya aikin soja a cikin shekaru 10 da suka wuce. Bikin ya nuna cewa, kasar Sin na raya aikin soja ba tare da boye kome ba. Haka kuma, jawabin da shugaba Hu ya yi ya nuna aniyar kasar Sin na ci gaba da bin manufar bude kofarta ga waje da kuma hada kai da samun wadatuwa.

Bayan da ya kalli bikin faretin sojan kasar Sin a ran 1 ga wata, Mark Regev, kakakin firayim ministan kasar Isra'ila ya taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Inda ya ce,"Cikin sahihanci gwamnatin Isra'ila da jama'ar kasar suna taya takwarorinsu na Sin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar. Isra'ila da Sin aminai ne. Ina fatan kasashen 2 za su iya kara inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakaninsu nan da shekaru da dama masu zuwa."

Kazalika kuma, a ganin Khaled Alaa El Dein, wakilin gidan rediyon wasannin motsa jiki na matasa na kasar Masar, bikin faretin sojan Sin yana da ban mamaki ainun! Yana mai cewar,"Na yi mamaki matuka da ganin bikin faretin soja da kasar Sin ta yi. A ganina, yanzu rundunar sojan kasar Sin ta riga ta zama daya daga cikin rundunonin soja mafi karfi a duk duniya. Suna mallakar sabbin makamai iri daban daban. Ana iya kwatanta karfin kasar Sin ta fuskar aikin soja da sauran kasashen duniya masu karfin aikin soja kamar Amurka. A yayin bikin faretin sojan, sojojin kasar Sin sun yi fice sosai kuma ana horar da su yadda ya kamata."

A ran 1 ga wata, jaridar Togo News ta fitar da wani sharhi a kan shafinta daya, inda ta ce, a cikin shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin ta samu ainihin babban ci gaba a fannoni daban daban. Dalilin da ya sa wannan kasa ta samu irin wadannan manyan sauye-sauye shi ne dukkan mutanen Sin suna yin kokari. Manyan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu sun sanya ta zama wata kasa mai karfi kuma mai yin babban tasiri, tana jawo hankalin kasashen duniya sosai.

Dadin dadawa kuma, a kasar Ghana, labaru game da murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin sun kasance cikin kanun labarun duniya kan manyan jaridun kasar a ran 1 ga wata. Jaridar Ghana Times ta wallafi littafin musamman domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin a ran 1 ga wata. Gidan talibijin din Metropolitan na Ghana ya nuna wani fim mai suna "kusantar kasar Sin" a daren ran 30 ga watan jiya.(Tasallah)