Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-09 16:17:08    
'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin sun samu karifn zuciya a Berlin

cri

Ran 23 ga watan jiya bisa agogon wurin, a bikin ba da lambobin yabo da aka yi a filin wasan Olympic na Berlin, a karo na farko an saurari taken kasar Sin. A rana ta karshe ta gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa ta shekarar 2009, 'yar wasa Bai Xue ta kasar Sin mai shekaru 21 da haihuwa ta samu lambar zinariya a cikin wasan gudun Marathon, wadda kungiyar 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ta dade tana neman samu. Ban da wannan kuma, sauran 'yan wasa Zhou Chunxiu da Zhu Xiaolin na kasar Sin sun zama na 4 da na 5, ta haka tawagar 'yan wasan gudun Marathon mata ta kasar Sin ta ci kofin duniya na wasan gudun Marathon, ta cimma burinta da ta yi shekaru da dama tana kokarin cimmawa. Lambar zinariya 1 da ta azurfa 1 da kuma ta tagulla 3 da kuma fintikau da 'yan wasan kasar Sin sabbin jini suka yi sun sanya kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ta sami karfin zuciya a yayin gasar fid da gwani ta kasa da kasa a wannan karo.

A matsayinsa na daya daga cikin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da suka fi ba 'yan wasa wahala, wasan gudun Marathon ya kan kawo wa 'yan wasa babbar barazana a jikinsu gami da tunaninsu. A cikin wasan gudun Marathon na gasar fid da gwani ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa da aka yi a birnin Berlin, Bai Xue, wadda a karo na farko ne ta shiga cikin gasar ta yi ta kasancewa cikin rukuni na farko, ta sheka da gudu kuma ta samu nasara a karshe, ta dauki jagoranci wajen wuce layin karshe da awoyi 2 da mintoci 25 da dakikoki 15. Ta kawo wa kasar Sin lambar zinariya daya kacal a yayin wannan gasa a Berlin.

Ko da yake wasu fitattun 'yan wasa ba su shiga gasar a wannan karo ba, amma lambar zinariya ta sanya Bai Xue ta nuna karfin zuciya sosai ga makomarta. Inda ta ce,"Ina farin cikin matuka. A gabannin layin karshe, 'yan wasa 2 kawai suke gudu a bayana, dan haka na kara tabbatar da burina, wato samun lambar zinariya. Ban fuskanci matsin lamba ba. Ina da karfin zuciyar samun wannan lambar zinariya. A ganina, ina da boyayyen karfi. Burina a yanzu shi ne zama zakara a gasar wasannin Olympic ta London."

1 2 3