Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-09 13:26:28    
Tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikaya aiki ne iri daya na kasashen Sin da Amurka

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an gudanar da dandlin tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikaya tsakanin kasashen Sin da Amurka a ranar 8 ga watan da muke ciki a birnin Phoenix yayin da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Wu Bangguo ke yin ziyara a kasar Amurka. A gun bikin bude dandalin, kasashen biyu sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa 41 da adadinsu ya kai kusan dolar Amurka biliyan 12 da miliyan 400. Mista Wu Bangguo ya yi lacca a gun bikin bude dandalin, inda ya furta cewa, tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka, wani aiki ne iri daya dake gabansu. Kana ya jaddada cewa, a yanzu haka dai, kamata ya yi kasashen biyu su nace ga bin ka'idar yin cinikaya cikin 'yanci da zummar magance ra'ayoyi iri daban-daban na bada kariya ga cinikayya.

Wannan dandalin tattaunawa ya janyo hankulan masu masana'antu fiye da 100 na kasashen biyu. Mataimakiyar ministan kasuwanci na kasar Sin Madam Ma Xiuhong da takwararta Madam Michelle O'Neill da kuma sauran jami'an da abin ya shafa sun halarci bikin bude dandalin. Mista Wu Bangguo ya yi lacca a gun bikin bude dandallin, inda ya fadi cewa, takardun hadin gwiwa 41 da aka rattaba hannu a kai sun kasance wani muhimmin sakamako ne na hadin gwiwar tatalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka, wanda aka samu a gun dandali tattaunawar har ma a daidai lokacin da ake fama da rikicin hada-hadar kudi na kasashen duniya. Yana mai cewa "A gun dandalin tattaunawar na yau, kamfanoni da masana'antu na kasashen biyu sun kuma kulla kwangiloli 41 dangane da fannin zuba jari da na hadin gwiwar tattalin arziki da fasaha da dai sauransu, wadanda adadinsu ya zarce dolar Amurka biliyan 12 da miliyan 400. Wannan dai ya sake shaida cewa, akwai dama da yawa da kasashen biyu suke da su na yin hadin gwiwa".

1 2 3