Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-08 16:32:08    
Daga wayar tarho zuwa wayar salula, sannan yanar gizo, sauye-sauyen da ake samu kan tsarin sadarwa cikin shekaru 60 da suka gabata a kasar Sin

cri
Madam Lu Suiying, mai shekaru 59 da haihuwa, da iyalinta suna zaune a wani gidan da aka gina yau fiye da shekaru 100 da suka gabata a shiyyar Xicheng ta birnin Beijing. A cikin shirinmu na yau, bari mu shiga wannan gida, mu yi hira da madam Lu Suiying da iyalinta kan sauye-sauyen da aka samu a fannin sadarwa cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata a gidanta domin sanin sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a fannin fasahohin bayanai a cikin shekaru 60 da suka gabata bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin.

Jama'a masu sauraro, abin da kuka saurara wata hira ce da aka yi a cikin wani fim mai suna "wayar salula" da aka nuna yau 'yan shekaru da yawa da suka gabata, kuma ya samu maraba sosai a kasuwa. A cikin wannan hira, an bayyana yadda aka samu wahala sosai lokacin da ake son buga waya ga iyali yau fiye da shekaru 40 da suka gabata. A cikin wannan murya, wani mutum yana son buga waya ga wani abokinsa da ke aiki a wata ma'aikatar hakar kwal. Da farko dai ya buga waya ga gidan waya, wani ma'aikacin gidan waya ya tambaye shi wane ne yake nema. Wannan mutum ya ce, yana son neman abokinsa da ke aiki a ma'aikatar hakar kwal mai lamba 3. Wannan ma'aikaci ya ba da amsa cewa, "Ina kula da wannan layin waya fiye da wata daya, ban taba samun nasarar kama hanyar waya zuwa ma'aikatar hakar kwal mai lamba 3 ba. Nisan da ke tsakanin nan zuwa ma'adinan hako kwal mai lamba 3 ya kai kilomita dari 2, akwai nisa sosai."

Madam Lu Suiying ta ce, wannan fim ya sa ta tuna da lokacin da take aiki a lardin Helongjiang, inda ke da nisan fiye da kilomita dubu 1 da birnin Beijing yau kusan shekaru 40 da suka gabata. Ta ce, a wancan lokaci, idan ta yi begen iyayenta da suke zaune a Beijing, babu sauran hanyar da za ta iya zaba, sai ta rubuta wasiku. Madam Lu Suiying ta ce, "A wancan lokaci, mun fi son wadanda suke aikewa da wasiku. Sabo da lokacin da masu aikewa da wasiku suka zo wurinmu, za mu iya samun wasiku daga iyalanmu. Musamman lokacin da muke aikin noma a kauyuka, kauyen da muke zaune yana da nisa sosai da gari. Mai aikewa da wasiku ya kan je kauyenmu sau daya a kowane sati."

A lokacin da take aiki a kauyen lardin Helongjiang, kamar yadda sauran Sinawa suke yi, idan ba ta da al'amari mai tsanani, shi ke nan, ba ta buga waya ga iyalanta da suke zaune a birnin Beijing. Sabo da a wancan lokaci, buga waya ba abu ne mai sauki. Ba a iya buga waya kai tsaye, kuma alamar waya ba ta da kyau, har ma wasu lokaci, ba a iya samun layin waya.

A farkon shekaru 80 na karnin da ya gabata, Lu Suiying ta samu izinin dawowa Beijing, kuma ta yi aure da wani Mr. Liu Xizhang. Amma mijinta ba ya aiki a Beijing. A wancan lokaci, yawan akwatunan wayar tarho sun yi kadan, kuma harajin waya ya yi tsada. Mr. Liu Xizhang ya tuna da cewa, "A wancan lokaci, dole ne mu rubuta batutuwan da muke son tattauna a cikin waya a kan wata takarda tukuna kafin mu soma buga waya. Ba ma iya yin hira kamar yadda muke yi a yanzu. Kuma harajin waya ya kai kudin Sin yuan 1 da digo 2 ga kowane minti daya, ya yi tsada kwarai. Ka sani albashinmu bai wuce kudin Sin yuan 30 da wani abu ba a kowane wata a wancan lokaci. Sakamakon haka, ba mu iya buga waya a kullum ba."

Ya zuwa karshen shekaru 80 na karnin da ya gabata, an soma sayar da wani irin wayar salular da surarta ta yi kama da wani tubali a kasuwar kasar Sin. A wancan lokaci, irin wannan kaya yana da daraja kwarai, kuma sai mutum mai arziki ne yake iya yin amfani da irin wannan wayar salula. Lokacin da take tunawa da yadda wani mutum ya yi amfani da irin wannan wayar salula mai kama da tubali, madam Lu Suiying ta ce, "Na ga wani mutum ya zo tare da wata wayar salula, muna jin mamaki sosai sabo da irin wannan waya ba ta da layi. Yanzu mun gane, ita ce wani irin wayar salula. Amma mun ji mamaki sosai a wancan lokaci."

Kafin wayoyin salula su samu karbuwa a duk fadin kasar, a tsakiyar shekaru 90 na karnin da ya gabata, yawan wayoyin da aka kafa su a gida ya samu karuwa cikin sauri. A shekara ta 2001, Liu Jingjin, wato diya ta farko ta madam Lu ta ci jarrabawar shiga jami'a. Iyayenta sun yaba mata, kuma sun sayo mata wata wayar salula a matsayin abin kyauta. Lokacin da ake amfani da wayoyin salulu, tun daga karshen karnin da ya gabata, matasa kamar yarinya Liu Jingjin sun soma yin amfani da injuna masu kwakwalwa da kuma kama kan yanar gizo. Liu Jingjin ta ce, a kan wata tashar neman abokan aji, ta samu abokan aji na makarantan firamare da ta sakandare da suka dade ba su sadu da juna ba. Liu Jingjin ta kara da cewa, a wancan lokaci, bayan da ta kama kan yanar gizo, abin farko da ta kan yi shi ne bude akwatin e-mail domin duba sabbin sakwannin da abokanta suka aika mata cikin farin ciki. Liu Jingjin ta ce, "A wancan lokaci, bayan da na tura wani sako ga wasu mutane, ina fatan su ba ni amsa da wuri. Bayan da na kama kan yanar gizo, ina fatan zan iya samun sabon sako domin sanin ra'ayoyinsu game da maganar da na yi a kan yanar gizo."

Yanzu, tsarin yanar gizo da wayar salula sun riga sun zama muhimman abubuwa a cikin zaman rayuwar jama'ar kasar Sin. Bisa "rahoton kididdigar da aka yi a karo na 24 game da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin yanar gizo" da gwamnatin kasar ta bayar a ran 16 ga watan Yuli, ya zuwa karshen farkon rabin shekarar da ake ciki, yawan mutanen da suke amfani da yanar gizo ya riga ya kai fiye da miliyan dari 3, wato yana kan gaba a duk duniya. A lokacin da take samun ci gaban yanar gizo, yawan mutanen da suke amfani da wayoyin salula ya kai kimanin miliyan 695, wato ko wadanne mutane biyu suna mallakar wayar salula daya.

Yanzu tsarin sadarwa mai sauki yana shafar zaman rayuwar jama'a daga dukkan fannoni. Yarinya Liu Jingting, kanwar Liu Jingjin ta ce, ba ma kawai yanar gizo da tsarin sadarwa na zamani suna bayar da gudummawa sosai wajen kara saurin daidaita harkokin ofis ba, har ma ta samu sauki lokacin da take hira da masoyinta. Liu Jingting ta ce, "Ni da masoyina mu abokan aiki ne. Ofishinsa yana hawa na farko, kuma ofishina yana hawa na uku. Amma muna da na'urar QQ irin ta yin hira kan yanar gizo a cikin ofishinmu, lokacin da muke aiki, mun iya kebe lokaci mu yi dan hira kan yanar gizo. Sannan, sabo da muna aiki a kamfani daya, mun iya buga waya ga juna ba tare da biyan harajin waya ba."

Bisa taimakawar 'ya'yansu mata biyu, madam Lu Suiying da mijinta Liu Xizhang sun kuma soma yin amfani da shafin intanet yau wasu shekarun da suka gabata. Idan ta samu lokaci, madam Lu ta kan karanta labaru kan shafin intanet, ko ta aika da sakwanni da hotuna ga abokanta. A waje daya, ba ma kawai mijinta Liu Xizhang ya san fasahohin yin amfani da wadannan fasahohi ba, har ma yana saya ko sayar da takardun hannun jari da sayen kayayyaki kan shafuffukan intanet. Kamar abincin kifaye da kayan kamun kifi su ne kayayyakin da ya kan saya ta hanyar yanar gizo.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, amfanin yanar gizo ya samu karfafuwa da kuma habaka a kasar Sin. Hukumomi daban daban na kasar Sin sun soma yin amfani da yanar gizo domin tabbatar da kwanciyar hankalin jama'a da ba da ilmi ga jama'a da kuma yin aikin tiyata ga marasa lafiya.

Jama'a masu sauraro, Yanzu, tsarin wayar salula da kasar Sin ke amfani da shi ya riga ya shiga wani sabon zamani na zuriya ta 3. A nan gaba, za a iya yin amfani da wayoyin salula domin samun kide-kide daga yanar gizo da kuma aikawa da takardu, har ma za a iya yin hira irin ta bidiyo kamar cikin halin fuska da fuska ta tsarin wayar salula na zuriya ta 3. Bugu da kari kuma, yanzu kamfanonin kasar Sin suna gaggauta yin nazarin fasahohi na tsarin wayar salula na zuriya na 4. (Sanusi Chen)