Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-13 16:07:09    
Zabiyar kasar Sin mai suna Song Song

cri

Kafin shekaru 3 da suka gabata, an kira wani bikin rera wakoki na musamman a kwalejin Gnesin's na Moscow. Dalibar kasar Sin Song Song ta rera wakokin da shahararrun masu tsara wakoki na duniya suka yi ta harshen Rasha, muryarta mai dadin ji ta samu maraba sosai daga kwararru a fannin kide-kide da 'yan kallon kasar Rasha. Wannan ne karo na farko da dalibar Sin ke iya yin bikin rera wakoki ita kadai a shahararren kwalejin kide-kide na kasar Rasha. Nan da shekara daya, Song Song wadda take a kasar Sin ta sake koma Rasha bisa gayyatar da aka yi mata don nuna wasan kwaikwayo na La Traviata.

An haifi Song Song a birnin Changsha na lardin Hunan dake kudancin kasar Sin, tana da shekaru fiye da 30 da haihuwa. Lardin Hunan lardi ne dake da wakokin kanannan kabilu da yawa, Song Song tana son rera wakoki da rawa sosai tun daga take wata yarinya, ban da wannan kuma, ta kan kwaikwayi shahararren mawaka da kyau, sabo da haka, ta shahara a wurinta. A wata rana, Song Song ta saurari wasan kwaikwayo na La Traviata a gidan malaminta, wannan wasan kwaikwayo shi ya canja rayuwarta. Song Song ta ce, "A lokacin da nake sauraron wasan kwaikwayo na La Traviata a karo na farko, ina fara kaunarsa, kuma na yi niyyar koyon fasahar rera waka a nan gaba, in akwai dama, zan nuna wasan kwaikwayo na La Traviata ni da kaina."

Song Song ta nuna fifiko sosai wajen rera waka, ta ci jarabawar shiga kwalejin koyon ilmin kide-kide na birnin Shanghai a yayin da ta gama karatu a makarantar midil. Kuma wannan kwaleji ya shahara sosai a kasar Sin. Song Song ta koyi ilmi daga wajen shahararrun malaman koyar da rera wake-wake na kasar Sin Wen Kezheng da Zhou Xiaoyan wadda aka mai da ita a matsayin koli a fannin rera waka na kasar Sin. Zhou Xiaoyan ta yi iyakacin kokarin horar da Song Song.

Song Song ta zama wata malama mai koyar da rera waka ta kwalejin koyon koyon ilmin kide-kide da wake-wake na Shanghai bayan da ta gama karatu, a sa'i daya kuma, ta rika rera wakoki da nuna wasannin kwaikwayo. Ta taba yin wasannin kwaikwayo tare da shahararrun mawakan kasar Sin Zhang Jianyi da Liao Changyong. A karshen shekarar 1996, gidan wasan kwaikwayo na Shanghai ya nemi mawaka don nuna wasan kwaikwayo na Carmen a duk fadin kasar Sin, Song Song ta dauki matsayin babbar jarumar wannan wasan kwaikwayo, ta nuna wasan kwaikwayo a karo na farko cikin rayuwarta ta harshen Faransanci.

1 2 3