Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-11 09:39:41    
Klaus Schlappner na da shaukin kasar Sin

cri

A karshen watan Mayu na wannan shekara, kungiyoyin wasan kwallon kafa na maza na kasashen Sin da Jamus sun yi kunnen doki a cikin wasan sada zumunci da suka yi a birnin Shanghai da ci daya da daya. Tawagar Jamus da ta zo kasar Sin ta hada da mutane 150 ko fiye, inda baya ga 'yan wasa da jami'an hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta Jamus da wakilan 'yan kasuwa, akwai wani tsohon abokin kasar Sin ta fuskar wasan kwallon kafa. Shi ne Klaus Schlappner, wanda ya taba zama babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin a shekarun 1990. A birnin Shanghai, wakilinmu ya yi hira da wannan tsoho dan kasar Jamus, wanda Sinawa masu sha'awar wasan kwallon kafa suke kaunarsa kamar yadda suke kaunar kakanninsu maza.

A lokacin da wannan tsoho mai shekaru 67 da haihuwa ya waiwayi kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da wasan kwallon kafa na kasar Sin, Mr. Schlappner ya ce,"Kasar Sin, wani muhimmin wuri ne matuka a gare ni. Ina kaunar wannan kasa, kuma ina kaunar wasan kwallon kafa na kasar Sin, balle ma Sinawa masu sha'awar wasan kwallon kafa. Na riga na hada zuciyata da wasan kwallon kafa na kasar Sin tare."

1 2 3