Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-28 21:04:02    
Hadin-gwiwar al'ummomin kasar Sin a jami'ar koyon ilimin likitanci ta Xinjiang

cri

Jihar Xinjiang ta Uyghur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, jiha ce ta hadin-gwiwar kabilu daban-daban, ciki kuwa har da Uyghur, da Kazakh, da Hui, da Mongoliya, da Xibo da dai sauran kabilu 13, wadanda suka shafe shekara da shekaru suna zama a can. A cikin tsawon lokaci, 'yan kananan kabilu daban-daban da na kabilar Han suna zama cikin lumana da kwanciyar hankali, haka kuma suna taimakawa juna a fannoni da dama. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu je jami'ar koyon ilimin likitanci ta jihar Xinjiang, mu ganewa idanu yadda dalibai 'yan kabilu daban-daban suke taimakawa juna, da zama tare cikin kwanciyar hankali.

Masu saurare, jami'ar koyon ilimin likitanci ta jihar Xinjiang dake cibiyar birnin Urumqi, jami'ar koyon ilimin likitanci ce mai fannonin karatu daban-daban wadda ke da dalibai sama da 13000, wadanda rabinsu 'yan kananan kabilu ne. Kwanan baya, bayan abkuwar mummunan tashin hankali a ranar 5 ga watan Yuli a birnin Urumqi, wakilin CRI yayi takanas har zuwa wannan jami'a, inda ya ganewa idonsa kome na tafiya cikin oda, haka kuma dalibai da malamai na kabilu iri-iri suna zama cikin kwanciyar hankali. Yayin da yake zantawa kan lamarin tashin hankali, wani dalibi dan kabilar Uyghur mai shekaru 21 da haihuwa, wanda ya shiga cikin jami'ar a shekara ta 2008, Yusufucan ya ce: "Da ba'a samu irin wannan tashin hankali ba a wurinmu. Ko da yake an yi mummunan tashin hankali a Urumqi a ranar 5 ga wata, amma zaman rayuwarmu a jami'a bai sauya ba, kome na tafiya cikin oda. Muna nan makaranta, muna kokarin karatu da share-fagen jarrabawa kamar yadda muke yi a da."

Dalibi na daban mai shekaru 23 da haihuwa, Ma Liang, wanda ya shiga cikin jami'a a shekara ta 2005, dan asali ne na jihar Xinjiang. Ya ce, 'yan a-ware a gida da waje dake karkashin jagorancin Rebiya Kadeer mai fafutukar kawowa kasar Sin baraka su ne suka tayar da tashin hankali da gangan, haka kuma yana fatan kasashen duniya zasu kawar da tunaninsu na cewa wai akwai sabani tsakanin kalibu daban-daban a jihar Xinjiang. Ma Liang ya ce: "Ba na tsammanin ana rashin zaman doka da oda a jihar Xinjiang, a ganina, jiharmu na cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Haka kuma, mutanen jihar suna son karbar baki, ina kaunar garinmu kwarai da gaske. A jami'armu, dalibai na kabilu daban-daban suna zama cikin hadin-gwiwa, haka kuma dalibai 'yan kananan kabilu da na kabilar Han su kan shirya bukukuwa da dai sauran ayyuka tare."

1 2 3