Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 22:06:09    
Bayani kan bukin Gexu a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin

cri

Yayin da yake zantawa kan tarihin rera waka, wani dan kabilar Zhuang mai suna Pan Lijin ya bayyana cewa:"Na fara rera waka ne tun lokacin da nike shekaru 18 da haihuwa, haka kuma na kara jin dadin rera wakoki. Lallai rera wakoki wata kyakkyawar al'ada ce ta kabilar Zhuang."

Masu saurare, a yankunan karkara, akwai matasa 'yan kabilar Zhuang da dama wadanda suka kulla zumunci ko soyayya ta hanyar rerawa juna wakoki. Wani mazaunin wurin mai suna Luo Guangli ya ce, wakokin da a kan rera tsakanin matasa 'yan kabilar Zhuang sun bayyana zumunta da soyayya a tsakaninsu. Luo Guangli ya ce:"Ta hanyar rerawa juna waka ne na kulla zumunci da soyayya da masoyiyata. A yankunan karkara, haka abun yake. Ta hanyar yin gasar rera waka ne, samari da 'yan mata suka kulla zumunci tare da juna."

Masu saurare, malam Bahaushe ya kan ce, "Gani ya kori ji". Muddin ka je gundumar Wuming ta jihar Guangxi, ka halarci bukin Gexu na 'yan kabilar Zhuang, za ka ji dadin wakokin da 'yan kabilar suka rera. Haka kuma, a cikin wakokin da su kan rera, 'yan kabilar Zhuang su kan sa ran alheri dangane da zaman rayuwarsu a nan gaba.


1 2 3