Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 10:50:19    
Gao Hongbo, sabon malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin

cri

Duk da haka, a ganin wakilinmu, wannan dan wasan gaba da ya taba jefa kwallo sau da yawa cikin ragar abokan karawa ya sha bamban da saura. Alal misali, wakilinmu ya tambaye shi da cewa, a tsakanin shahararrun malaman horas da wasanni na kasa da kasa, wane ne ya fi kaunarsa. Ba tare da tunani cikin dogon lokaci ba nan da nan Gao Hongbo ya amsa cewa, ba shi da irin wannan mutum. Yana koyon fasahohin wadannan shahararrun malaman horas da wasanni ne kawai. Yana mai cewar,"Ana bin mabambantan hanyoyi ne wajen yin wasa da kwallon kafa. Malaman horas da wasanni masu tarin yawa sun samu nasara. Ina son in koyi dukkan fasahohi daga wajensu. Tare da fahimtata kan irin wannan wasa, ina fatan kasar Sin za ta bi hanyar raya wasan kwallon kafa da ke dacewa da ita."

Irin wannan gajeriyar amsa ta cancanci halayyar Gao Hongbo sosai. Bayan goman shekaru, Gao Hongbo bai sauya halayyarsa ko kadan ba, haka kuma bai yi watsi da rubuta littafin tsarin lokaci kan aikin horaswa a ko wace rana ba. Gao Hongbo ya gaya wa wakilinmu cewa, tun lokacin da shekarunsa suka kai 12 da haihuwa da ya fara yin wasa da kwallon kafa, har zuwa yanzu, a ko wace rana, yana rubuta littafin tsarin lokaci kan aikin horaswa. Inda ya ce,"Rubuta littafin tsarin lokaci kan aikin horaswa, aikin gida ne da nake yi a ko wace rana, kuma ya zama tilas ne a gare ni."

Littafin tsarin lokaci mai girma cike yake da kaunar da Gao Hongbo yake yi wa wasan kwallon kafa, haka kuma, ya shaida mana yadda wannan tsohon dan wasan gaba na kungiyar kasar Sin ya zama babban malamin horas da wasanni mafi kuruciya a cikin hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin, wanda kuma kungiyarsa ta zama zakara, a yanzu kuwa, ya zama babban malamin horas da wasanni mafi kuruciya a tarihin kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin. A ganin kowa, kuruciya na da matsayin alama mafi muhimmanci ga Gao Hongbo. Sa'an nan kuma, ana shakkar karfinsa a sakamakon kuruciyarsa. To, yaya ra'ayinsa game da wannan? Gao Hongbo ya gaya mana ra'ayinsa da cewa,"Ma'anar kuruciya ita ce kokarin yin koyi da kome da kome da kuma rashin nuna girman kai. In kana da kuruciya, to, dole ne ka san ra'ayoyin kowa da kowa, ta haka kana iya samun wata hanyar da ta fi dacewa dan samun ci gaba."

1 2 3