Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-30 23:06:02    
Zagayawa a farfajiyar da za a yi taron baje-koli na kasa da kasa a shekarar 2010 a birnin Shanghai

cri

Huang Jiangzhi, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin taron baje-koli na duniya na Shanghai ya yi mana karin bayani kan wannan gini mafi girma a farfajiyar taron baje-koli na duniya na Shanghai, inda ya ce,"Mun yi amfani da fasahar zamani domin shigar da hasken rana zuwa banayensa 2 a karkashin kasa, ta haka, mutane za su iya daukar kansu kamar suna kan doron kasa, a maimakon a karkashin kasa, za su iya ganin hasken rana."

A cikin gine-ginen din din din guda 4, cibiyar nuna wasanni ta fi nuna halin musamman ta fuskar fasaha. Mutane sun sifanta ta da tamkar wani bawo. Zhang Xi, wadda ke yi wa matafiya karin bayani ta yi bayani da cewa,"Wannan gini mai surar bawo shi ne cibiyar nuna wasanni. Yana da kyan gani sosai a lokacin da aka haskaka ta da dare. Halin musamman mafi girma da take da shi shi ne sauya yawan kujeru bisa yawan 'yan kallo. 'Yan kallo 4000 zuwa 18000 za su iya jin dadin kallon wasanni a lokaci guda."

Kazalika kuma, domin kara yin bayani kan babban taken taron, a cikin farfajiyar taron baje-koli na duniya na Shanghai, za a gina dakin nune-nune na musamman domin tattaunawa kan dangantaka a tsakanin birane da mutane da rai da kuma taurari da kuma abubuwan da za su auku a nan gaba, inda kuma za a kebe bangarori 2 a ciki bisa tunanin yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli. Madam Zhang ta ci gaba da cewa,"A rufin wannan dakin nune-nunen babban taken taron, mun yi amfani da fasahar zamani, mun gina wasu 'yan kananan kwari, ta haka za a iya tattara ruwan sama, za a iya yin ban ruwa ga tsirran da ke kusa da wannan gini kai tsaye."

Cibiyar taron baje-koli na duniya ita ce gini na karshe da ke cikin gine-ginen din din din 4, da muka ambata a baya. A shekara mai zuwa, za ta kasance cibiyar watsa labaru da kuma karbar baki.

A gaskiya, daya daga cikin muhimman makasudai 2 da taron baje-koli na duniya na Shanghai ya tsara shi ne jawo hankalin mutane kimanin miliyan 70 da su halarci taron. Shi ya sa a cikin farfajiya mai fadin murabba'in kilomita 5.28, yadda za a warware matsalar zirga-zirgar mutane masu yawan haka yake da muhimmanci matuka. Madam Diao ta gaya mana cewa,"A kewayen farfajiyarmu, akwai hanyoyin jirgin kasa guda 5. A dab da babbar gadar Lupu, mun shimfida hanyar jirgin kasa mai lamba 13, wadda ita ce hanyar jirgin kasa ta musamman domin taron baje-koli na duniya. A cikin watanni 6 da ake shirya taron, za a yi amfani da wannan hanyar jirgin kasa ta musamman domin taron ne kawai. Bayan rufe taron, za a tsawaita hanyar. Bugu da kari kuma, a cikin farfajiyarmu, za mu samar da tasoshin jiragen ruwa guda 3, ta haka mutane za su iya kaiwa da komowa a tsakanin gabobi na yamma da gabas na kogin Huangpujiang domin halartar taron baje-koli na kasa da kasa na Shanghai."


1 2 3