Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-29 17:01:31    
Lardin Jilin yana kokarin farfado da masana'antu

cri

Ya kasance tamkar daya daga cikin muhimman kamfanonin samar da kayayyakin jirgin kasa a kasar Sin, yawan jiragen kasa da kamfanin kera jiragen kasa na Changchun ya samar ya kai kashi 50 cikin kashi dari bisa na jimillar jiragen kasa na kasuwar kasar Sin. A waje daya, lokacin da ake raya tsarin kananan jiragen kasa cikin sauri a biranen kasar Sin a cikin 'yan shekarun baya, wannan kamfani ya kuma samu kwangiloli da yawa. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kananan jiragen kasa da kamfanin ya samar wa birane daban daban ya kai kashi 80 cikin kashi dari bisa na dukkan kananan jiragen kasa da ake amfani da su.

A lokacin da yake kara karfin nazarin sabbin fasahohin zamani da kansa, kamfanin kera jiragen kasa na Changchun ya kan shigo da fasahohi da injunan zamani daga kasashen waje a kai a kai. Bayan da aka harhada su, fasahohin zamani da ake amfani da su a cikin aikin hada jiragen kasa da aka kera a kamfanin kera jiragen kasa na Changchun yana kan matsayi mai rinjaye a duk duniya. Mr. Zhang Dongli ya gaya wa wakilinmu cewa, jiragen kasa, ciki har da taragun fasinjan jirgin kasa da kananan jiragen kasa da kamfaninsa ya samar sun samu karbuwa a kasashe da dama. Mr. Zhang Dongli ya ce, "Mun riga mun fitar da taragun fasinjan jirgin kasa da muka kera a kasashen Australiya da Thailand da Pakistan da yankin Hongkong na kasar Sin da sauran yankunan duniya. Yawan jiragen kasa da muke fitar da su zuwa kasashen waje ya kai sulusi bisa dukkan jiragen kasa da muke kerawa. Yanzu yawan kwangilolin da muka samu daga kasashen waje yana ta karuwa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne muna amfani da fasahohin zamani da yawa a cikin kayayyakin da muke kerawa."

Mr. Zhang Dongli ya kara da cewa, sabo da kamfaninsa yana da karfin yin takara a fannonin fasahohi da yawan kudin da aka kashe domin samar da kayayyaki, rikicin kudin na duniya kusan bai haddasa illa ga harkokin kamfaninsa ba.

Dadin dadawa, lardin Jilin lardi ne da ke bunkasa masana'antun motoci. An samar da motar farko ta kasar Sin ne a kamfanin farko na kera motoci na kasar da ke birnin Changchun. Bisa manufofi an alfarma da aka bayar domin farfado da tsohon sansanin masana'antu na yankin arewa maso gabashin kasar Sin, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kamfanin farko na kera motoci na kasar Sin da ke birnin Changchun ya kara mai da hankali kan ayyukan kirkiro sabbin fasahohin zamani da kansa da kuma bunkasa karfin takara mafi muhimmanci na kamfanin. Mr. Bai Yu wanda ke kula da kamfanin samar da kananan motoci mai hannun jari na kamfanin farko na kera motoci na kasar Sin, ya bayyana cewa, "Muna da hanyoyin zamani na kera motoci, kuma muna namijin kokarin yin amfani da injunan zamani domin rage kudin da muke kashewa da kuma kara karfin yin takara na kayayyakinmu a kasuwa."

1 2 3