Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 13:52:52    
Saurayi mai bakar fata da ke cikin kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Sin

cri

Yanzu mambobin sabuwar kungiyar wasan kwallon raga wato volleyball ta maza ta kasar Sin suna samun aikin horaswa tare a nan Beijing domin share fagen gasar fid da gwani ta wasan kwallon raga ta maza ta nahiyar Asiya da za a yi a watan Agusta na wannan shekara. A cikin wannan kungiya, wani saurayi ya fi jawo hankalin jama'a. Wannan saurayi mai bakar fata na da curarriyar suma, da lebe mai kauri da kuma fararen hakora. A ganin wasu, shi ne wani dan wasa mai bakar fata daga kai zuwa kafa. Mene ne dalilin wani mai bakar fata ya bullo a cikin kungiyar kasar Sin? Yau ma za mu yi muku bayani kan dalilin da ya sa wannan saurayi mai bakar fata ya bayyana a cikin kungiyar wasan kwallon raga ta kasar Sin.

A filin aikin horaswa da kungiyar wasan kwallon raga ta maza ta kasar Sin take yin amfani da shi, wani saurayi ya fi nuna kuzari. A wani lokaci, ya tsalle tare da jefa kwallo ta ketare raga, a wani lokaci ma, ya kan murgina domin kare kwallo. Ya iya sarrafa jikinsa kwarai da gaske, kuma cike yake da karfi da kuzari. Sunansa shi ne Ding Hui, wani dan wasan musamman ne a filin wasan kwallon raga da bai iya kai hari ba, sai kare kwallo kawai. A karo na farko ne aka saka sunansa cikin jerin sunayen mambobin sabuwar kungiyar kasar Sin. Dalilin da ya sa Ding Hui ya jawo hankalin mutane cikin sauri shi ne domin siffarsa, a maimakon fasaharsa. A ganin wasu, da an gan shi, sai an dauki wannan saurayin da ke da bakar fata da curarriyar suma da kuma lebe mai kauri tamkar dan wasan da ya zo daga kasashen Afirka. Amma babu shakka a cikin kungiyar kasar Sin, ba zai yiwu ba a shigar da dan wasa baki a ciki. A gaskiya, a matsayin barbarar 'yan yawa, wanda iyayensa suka zo daga kasashen Afirka da Sin, Ding Hui ya girma ne a nan kasar Sin, wani tsantsar Basine ne.

1 2 3