Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-02 09:55:42    
Ana neman sabuwar hanyar bunkasa bikin baje koli na Guangzhou

cri

A ran 7 ga watan Mayu, an rufe bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na kasar Sin a karo na 105 a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar.

An soma yin wannan biki ne tun daga shekarar 1957. A kan shirya shi sau biyu a kowace shekara, wato a kan shirya wani a lokacin bazara, kuma a kan shirya wani daban a lokacin kaka. A gun wannan bikin da aka shirya a lokacin bazara na shekarar da ake ciki, 'yan kasuwa da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da dari biyu sun halarci wannan biki, wato ya ragu da kashi 5 cikin kashi dari. Yawan kudin cinikayya da aka yi a yayin bikin ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 26, wato ya ragu da kashi 17 cikin kashi dari.

Ko da yake har yanzu ana yakar rikicin kudi na duniya, amma bai haddasa illa sosai ba ga bikin cinikin kayayyakin da ake shige da fice na kasar Sin da ake yi a birnin Guangzhou. Sabo da a yayin wannan biki, an dauki wasu matakan yakar rikicin kudi na duniya. Alal misali, an samar da takardun gayyata ga 'yan kasuwa dubu dari 8 da suke zaune a duk fadin duniya. A waje daya, lokacin da ake gayyatar muhimman 'yan kasuwa, an kuma gayyaci 'yan kasuwa da yawa daga kasashen Gabas na Tsakiya da Turai na Tsakiya da Afirka da Indiya da kuma yankunan kudancin Amurka.

1 2 3