Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-13 19:06:52    
Jama'ar lardin Sichuan suna ta farfadowa daga tsoron girgizar kasa

cri

Masu sauraro, sautin da kuka saurara dazun nan ihu ne da 'yan makarantar firamare ta garin Jiebei na birnin Mianyang da ke lardin Sichuan na kasar Sin suka yi don ba da kwarin gwiwa ga wadanda suka jikkata sakamakon girgizar kasa da ta auku yau da shekara guda da ta gabata.

Ba kawai mutane sun ji raunuka ko sun nakasa sakamakon girgizar kasa ba, hatta ma an sheda samun illa sosai ga lafiyar tunaninsu. Lu Tao da ke gudanar da aiki a wata masana'antar samar da siminti ta gundumar Beichuan ya gaya wa wakilinmu cewa, dansa ya kan yi mugun mafarki sakamakon ganin mutuwar abokan karatunsa a cikin bala'in girgizar kasa. Ya ce,

"Lokacin aukuwar girgizar kasa, dana yana karatu a ajin farko na makarantar sakandare ta gundumar Beichuan. Bayan da shi kansa ya fito daga kangwaye, ya sake shiga makarantar domin ceton abokan karatunsa, amma bayan da suka samu nasarar fita daga kangwaye, 2 daga cikin wadannan dalibai 3 sun mutu. Don haka a cikin dogon lokaci, na kan kasance tare da shi yayin da yake yin barci. Kullum ya kan ji tsoro, har ma ya kan yi kuka sakamakon mugun mafarki, ya gaya mini cewa, ya kan ga abubuwan da ke da jini da yawa a cikin mafarkinsa."

Bayan aukuwar girgizar kasa, ma'aikatar kiwon lafiya da manyan asibitoci daban daban na kasar Sin sun aika da kungiyoyin ba da taimako kan kyautata tunani zuwa yankuna da suka yi fama da girgizar kasa domin yi wa jama'a jiyya a fannin tunani, kuma sun mai da hankali sosai kan matasa da kuma iyayen da yaransu suka mutu. Ya zuwa yanzu, ana gudanar da wani aikin nazari kan yin jiyya a fannin tunani bayan girgizar kasa a yankuna da suka yi fama da girgizar kasa. Kuma an kiyasta cewa, ya zuwa shekara ta 2010, za a kafa wani tsarin jiyya a wannan fanni domin ci gaba da lura da lafiyar tunanin jama'a da suka shafu fama da girgizar kasa.

Cai Li, mataimakin shugaban asibitin jama'ar lardin Sichuan ya bayyana cewa, bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, aikin jiyya a fannin tunani da asibitin ya yi ya samu kyakkyawan samakamko. Ya ce,

"Mun gudanar da aikin jiyya a fannin kyautata tunani cikin yakini. Mun kafa kungiyar jiyya a fannin kyautata tunani ba tare da bata lokaci ba bayan girgizar kasa domin ba da shawarwari kan lafiyar tunani da kuma kyautata tunanin jama'a. Ban da wannan kuma mun shirya kwasa-kwasai har sau hudu don horar da fasahohin ba da taimako kan kyautata tunanin wadanda suka jikkata da kuma masu aikin jiyya. Ya zuwa yanzu, mun riga mun yi jiyya ga mutane 697 a wannan fanni. Wadanda suka jikkata suna iya kwantar da hankalinsu yanzu da kuma tinkarar hakikanan abubuwa yadda ya kamata."

Lu Tao da muka ambata a baya ya gaya mana cewa, ta hanyar yin jiyya a fannin tunani, yanzu halin da dansa ke ciki ya samu kyautatuwa sosai.

Masu sauraro, sautin da kuke saurara yanzu waka ce mai taken "Gidanmu"da Niu Yu, wata 'yar makarantar firamare da ta shafu daga girgizar kasa ta rubuta don gidajen da suka lalace sakamakon girgizar kasa. A cikin wannan bala'in, Niu Yu ta rasa kafarta ta dama. Amma ba ta bata ranta ba, bayan da ta samu jiyya ta tsawon watanni biyu, yanzu tana iya sake yin wasan kwallon tebur a tsaye tare da taimakon kafar roba.

Kamar yadda Niu Yu ke yi, yanzu dimbin nakasassun mutane da suka shafu daga girgizar kasa suna iya yin wasannin motsa jikunansu, ta abubuwan da suke yi, suna fatan nuna cewa, suna farfaduwa daga tsoron girgizar kasa, kuma ba za su nuna gazawa ba sakamakon haduwa da bala'i daga indallahi.(Kande Gao)