Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-13 16:35:48    
Hukumomi na gwamnatoci bisa matsayi daban daban na lardin Sichuan sun sa himma domin daukar matakai

cri
Babbar girgizar kasa da ta auku a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, mutane da yawa sun ji rauni, wasu sun rasa rayuka sakamakon hadarin, bayan haka kuma an yi hasarar dukiyoyi masu yawa. A matsayinsa na wani muhimmin wurin da ya fi samun jarin waje a yammacin kasar Sin, ko wannan babbar girgizar kasa za ta kawo mumunan tasiri ga zuba jarin waje a lardin Sichuan, ko a'a? A lokacin cika shekara daya da aukuwar girgizar kasa, wakilinmu ya kai ziyara ga wasu masana'antun kasashen ketare da ke Lardin Sichuan, don fahimtar halin gudanar da harkokinsu. An gano cewa, tun shekara daya da ta wuce, hukumomi na gwamnatoci bisa matsayi daban daban na lardin Sichuan sun sa himma domin daukar matakai, ta yadda suke taimakawa masana'antu masu jarin waje ta fuskar kawar da tasirin da girgizar kasa ta haddasa, da kuma kara kwarin gwiwar zuba jari a lardin Sichuan. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani kan wannan.

Kebabben wurin kafa masana'antun da ke yin amfani da sabbin fasahohi na zamani dake birnin Chengdu a lardin Sichuan yana daya daga cikin tsofaffin kebabbun wuraren kafa masana'antun da ke yin amfani da sabbin fasahohi na zamani bisa matsayin kasa, shi ne kuma wurin da masana'antu masu jarin waje suke tattare cikinsa a lardin Sichuan. Shahararrun masana'antun ketare fiye da 400 sun kafa kamfanoninsu a nan. Kamfanin Ericsson ya kasance daya ne daga cikinsu. Babban manajan kamfanin Ericsson da ke birnin Chengdu Mr. Kong Xiandong ya bayyana cewa, 'An kafa cibiyar nazari ta kamfanin Ericsson da ke birnin Chengdu a shekarar 2004. Dalilan da suka sa muka zabi birnin Chengdu don kafa cibiyar su ne, da farko, mun samu goyon baya sosai daga gwamnatin birnin, na biyu, mun iya samun ma'aikata masu inganci a nan. Bayan haka kuma, yawan kudaden da muka kashe wajen zuba jari a birnin Chengdu kadan ne idan an kwatanta da biranen Shanghai, da Beijing, da kuma sauran birane na kasar Sin.'

Manyan gine-gine na birnin Chengdu sun jure wa jarrabawa daga babbar girgizar kasa, dan haka, masana'antun ketare sun kara samun imani kan zaben da suka yi a da na zuba jari a birnin. Shugaban kamfanin UBSOFT na Chengdu, wani shahararren kamfanin raya manhaja Mr. Cao Jianwei ya gaya mana cewa, 'Manyan gine-gine masu inganci wani muhimmin dalili ne da ya sa muka zabi Chengdu don zuba jari. Manyan gine-gine na birnin sun jure jarrabawa daga girgizar kasa da ta auku a watan Mayu na shekarar da ta wuce. A lokacin faruwar girgizar kasa, muna aiki a ofisoshinmu, a lokacin kuma, an samar da wutar lantarki kamar yadda ya kamata, bayan haka kuma, ba a gamu da matsaloli kan internet ba. Wannan na nuna cewa, ya yi daidai da muka zuba jari a Chengdu.'

A lokacin da wakilinmu ke yin ziyara, ya gano cewa, dalilin da ya sa masana'antu da suka zuba jari ba su janye jiki daga lardin Sichuan ba, har ma suna ta kara zuba jari a birnin, shi ne domin gwamnatoci bisa matsayi daban daban na lardin sun dauki matakai daban daban, don rage mugun tasirin da bala'in girgizar kasa ya kawo wa masana'antu masu jarin waje, bayan haka kuma, sun mayar da kara kwarin gwiwar zuba jari ga 'yan kasuwa na kasashen ketare a matsayin wani muhimmin nauyin da ke kansu a cikin ayyukan sake gina lardin.

Wani jami'in hukumar cinikayya ta lardin Sichuan Mr. Sheng Zhenghua ya ce, 'Ayyukan zuba jari da 'yan kasuwa na kasashen ketare suka yi, wadanda yawan kudinsu ya wuce dalar Amurka miliyan 10 a watanni uku na farkon shekarar 2009 a lardin Sichuan sun kai 15. 'Yan kasuwa na ketare suna ta kaunar zuba jari a lardin Sichuan."