Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-12 17:30:35    
Kyakkyawan lardin Sichuan tana yin marhabin da matafiya

cri
Tun fil azal yanzu lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin ya shahara ne bisa albarkatun yawon shakatawa. Amma mummunar girgizar kasa da ta auku a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 ta kawo wa lardin Sichuan cikas game da kudaden shiga daga hannun matafiya. A matsayinsa na daya daga cikin ginshikan Sichuan, an yi asarar yuan biliyan 60 ko fiye daga aikin yawon shakatawa kai tsaye. A sakamakon kokarin da ake yi a cikin kusan shekara guda da ta wuce, yanzu akwai alamar farfadowar aikin yawon shakatawa a wuraren da girgizar kasa ta shafa a lardin Sichuan.

Aotani Yushi, wani matafiyin da ya zo daga kasar Japan ya sha zuwa nan kasar Sin. Bayan aukuwar girgizar kasa a lardin Sichuan a ran 12 ga watan Mayu na shekarar bara, domin nuna girmama ga al'adun gargajiya na kasar Sin ya sake zuwa shiyyar yawon shakatawa ta madatsar ruwa ta Dujiangyan da bala'in ya lalata ta kwarai da zummar ganin halin da wannan shiyya ke ciki. Yanzu yanayi na kwanciyar hankali ta fuskar yawon shakatawa a wurin ya faranta ransa sosai, inda ya ce,"Ina sha'awar tarihin kasar Sin. Na fara karanta littattafan tarihi game da kasar Sin tun ina karami. Wannan shi ne karo na 6 da na zo nan kasar Sin. Bayan da na yi ritaya, na kan zo wannan kasa a ko wace shekara. Na kan yi makwanni 3 zuwa 4 ina zaune kasar a ko wane karo. A wannan karo ma, ban ga gidaje da yawa da suka rushe a sakamakon bala'in ba. Kamfanin yawon shakatawa na Japan ya gaya mini cewa, an samu kwanciyar hankali a nan, shi ya sa na zo nan ziyara cikin kwanciyar hankali."

A shiyyar yawon shakatawa ta madatsar ruwa ta Dujiangyan, akwai matafiya da yawa kamar Mr. Aotani. Bala'in da aka samu a shekarar bara ya lalata wasu wurare a wannan shiyya. Ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar bara, an sake bude kofar wannan shiyya ga matafiya. Zhang Zhongsheng, wani jami'in sashen harkokin kasuwanni na hukumar yawon shakatawa ta birnin Dujiangyan ya yi karin bayani da cewa,"Ya zuwa karshen watan Maris na wannan shekara, bisa kididdigar da muka samu a fannonin yawan matafiyan da muka karba da kudin shiga daga hannunsu a farkon watanni 3 na wannan shekara, ma iya cewa, aikin yawon shakatawa a birninmu ya sami kyautatuwa yadda ya kamata. Yawan matafiya da kudin shiga sun kusan yi daidai da na makamancin lokaci na shekarar bara. Muna da karfin zuciya wajen farfado da aikin yawon shakatawa zuwa yadda ya taba kasancewa a shekarar 2007 kafin karshen wannan shekara."

Domin farfado da aikin yawon shakatawa a wuraren da bala'in ya shafa cikin sauri, jim kadan bayan aukuwar bala'in, an fara gaggauta yin kwaskwarima kan na'urori da hanyoyin da bala'in ya lalata a shiyyoyin yawon shakatawa a lardin Sichuan. Bugu da kari kuma, hukumomin yawon shakatawa a wurare daban daban sun fitar da kananan littattafai kan hanyoyin yawon shakatawa a wuraren da bala'in ya shafa, ciki har da ni'imtattun wurare a wurin da na'urorin sufuri da na karbar matafiya, su rarraba su a otel-otel da tasoshin motoci. Matthias Jaehrling ya bayyana cewa,"Na sha ganin hotuna game da wuraren da bala'in ya shafa, haka kuma, na taba ganin gidajen da bala'in ya lalata a birnin Dujiangyan. Amma yanzu a galibi ba mu iya ganin alamun girgizar kasa ba. An sami saurin ci gaba wajen sake gina wannan birni."

Baya ga shiyyar yawon shakatawa ta madatsar ruwa ta Dujiangyan, shahararren kwarin Jiuzhaigou da ke cikin gundumar Nanping a yankin kabilun Qiang da Tibet na Aba mai cin kashin kansa ya samu farfadowa sosai. Xiao Youcai, mataimakin shugaban yankin Aba ya yi karin bayani da cewa, ko da yake bala'in bai raunana galibin muhimman na'urorin yawon shakatawa a kwarin Jiuzhaigou ba. Amma ya lalata hanyoyin mota na zuwa kwarin, ta haka yawan matafiyan da su kan je kwarin Jiuzhaigou ziyara ya dan ragu. Mr. Xiao yana mai cewar,"Matakan da muka dauka a yanzu su ne da farko gaggauta kawar da shinge a kan hanyoyin zuwa arewa maso yammacin kasarmu, ta haka matafiya za su iya zuwa kwarin Jiuzhaigou daga birnin Lanzhou na lardin Gansu cikin mota kai tsaye. Na biyu shi ne yin shirin mika rahoto ga babbar hukumar zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar Sin domin shimfida hanyoyin jiragen sama daga Beijing da Shanghai da Shenzhen da Tianjian da sauran manyan birane zuwa kwarinmu. Dan haka, yawan matafiyan da za mu karba zai karu sosai."

Mr. Zhang ya kuma kara da cewa, yanzu yawan matafiyan da su kan yi ziyara a kwarin Jiuzhaigou ya kai 3800 a ko wace rana. An samu alamar kyautatuwa. Inda ya ce,"Mun riga mun kammala ayyukan maido da muhimman ayyukan yau da kullum da aka dan lalata su. Shi ya sa yanzu matafiya suna iya samun kwanciyar hankali a lokacin da suke yin ziyara a kwarinmu na Jiuzhaigou da shiyyar yawon shakatawa ta Huanglong da kuma babban filin ciyayi."

Da fatan dai sa kaimi kan farfado da aikin yawon shakatawa a lardin Sichuan, hukumar yawon shakatawa ta lardin ta yi kira ga shiyyoyin yawon shakatawa da ke duk fadin lardin da su hada kansu, su bai wa matafiya gatanci, su kuma shirya harkar musamman a watan Mayu domin nuna godiya ga wadanda suka taba bai wa lardin Sichuan taimako, ta haka za a iya karfafa gwiwar karin matafiya da su kashe karin kudade a shiyyoyin.

Kazalika kuma, kamfanonin yawon shakatawa da dama a lardin Sichuan sun fito da sabbin hanyoyin yin ziyara domin jawo hankalin karin matafiya, kamar yin ziyara a kauyukan lardin Sichuan.

A sakamakon ayyukan sake gina lardin na tsawon shekara guda, yanzu an farfado da aikin yawon shakatawa yadda ya kamata a lardin Sichuan, musamman ma a cikin shekarar da muke, lardin Sichuan ya samu saurin farfadowar aikin yawon shakatawa bisa sake gina muhimman na'urorin yawon shakatawa da kuma yin kiran kasuwannin yawon shakatawa. A lokacin da yake zantawa da wakilinmu, Zhang Gu, shugaban hukumar yawon shakatawa ta lardin Sichuan ya gaya mana cewa, "A sakamakon yunkurin sake gina lardin na tsawon shekara guda, a cikin farkon watanni 3 na wannan shekara, mun sami kyakkyawan ci gaba. Jimilar kudaden shiga ta fuskar yawon shakatawa ya karu da kashi 12.1 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara, a wancan lokaci ba mu sami bala'in girgizar kasa ba tukuna."

Mr. Zhang ya ci gaba da cewa, yanzu lardin Sichuan na samun saurin ci gaban aikin yawon shakatawa a sakamakon matakan farfadowa da ake dauka bayan aukuwar bala'in. Ya nuna karfin zuciya sosai ga farfadowar aikin yawon shakatawa a lardin Sichuan daga dukkan fannoni. Yana mai cewar,"Muna da karfin zuciya wajen samun kudaden shiga da yawansu ya wuce yuan biliyan 121.7 daga aikin yawon shakatawa. Mun taba samun irin wannan adadi a sheakrar 2007."

Karfin zuciyar da mazauna lardin Sichuan suke nunawa wajen sake gina garinsu tana inganta karfin zuciyar matafiya sannu a hankali. Farfadowar kasuwar yawon shakatawa tana kuma ba da tabbaci wajen samun irin wannan karfin zuciya. Kyan ganin surar lardin Sichuan ikon Allah ne. Mun yi imani da cewa, bayan bala'in girgizar kasa, lardin Sichuan zai yi marhabin da baki daga sassa daban daban na duniya bisa yanayin da yake da shi mai kyau.(Tasallah)