Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-24 22:20:04    
Taron kolin G20

cri
Masu sauraro, kwanan nan, me ya fi daukar hankulanku? Watakila za ku ce, taron kolin G20 da aka yi a birnin London, inda shugabannin kasashe na G20 suka zauna tare suka yi shawarwari a kan yadda za a tinkari matsalar kudi da kasashen duniya baki daya ke fama da ita, ya fi jawo hankulanmu. Haka ne, hasali ma dai, taron ya jawo hankulan kasashen duniya baki daya. Sabo da haka, a farkon shirinmu na yau, zan amsa wasu tambayoyin masu sauraronmu game da taron. Da farko dai, tambaya da zan amsa ta fito daga hannun Dalhatu Yusuf, a Maiduguri, jihar Borno, tarayyar Nijeriya, wanda a cikin sakonsa na Email, ya tambaya, "shin wadanne kasashe ne ke cikin kungiyar nan da aka san ta da sunan G20?"

To, malam Dalhatu Yusuf, mun gode maka da aiko mana wannan tambayar. Kungiyar G20, wato Group 20, ko kuma kungiyar kasashe 20, ta kafu a ran 25 ga watan Satumba na shekarar 1999, kuma tana kunshe da kasashe 20, ciki har da Amurka da Japan da Jamus da Faransa da Birtaniya da Italiya da Ganada da Rasha, wadanda ke cikin kungiyar G8, ban da su kuma, akwai Sin da Argentina da Australia da Brazil da Indiya da Indonesia da Mexico da Saudiyya da Afirka ta kudu da Koriya ta kudu da Turkiya da kuma tarayyar Turai. Dalilin da ya sa aka kafa kungiyar shi ne, bayan matsalar kudi da ta galabaitar da kasashen Asiya a shekarar 1997, gamayyar kasa da kasa suka fara gane cewa, domin cimma burin daidaita matsalar kudi ta duniya, ya zama dole kasashen duniya su sanya hannayensu baki daya, sabo da haka, a watan Satumba na shekarar 1999, ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashe 7 masu karfin tattalin arziki na yammaci, sun ba da sanarwa, inda suka yarda da kafa kungiyar G20 da ke kunshe da manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na yammacin duniya da kuma kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa, don su yi shawarwari kan gyaran tsarin kudi na duniya.

To, amsarmu ke nan ga tambayar malam Dalhatu Yusuf, wanda ya zo daga Maiduguri, jihar Borno, tarayyar Nijeriya, da fatan ta taimaka wajen fadakar da masu sauraronmu a kan G20.

Har wa yau kuma, Mohammed Idi Gargajiga, daga Gombawa CRI Listeners Club, Jeka da fari Quarters, Gombe, tarayyar Nijeriya, ya ce, "Domin jin dadin wannan shiri a kowace ran juma'a ina so wannan fili ya amsa mini tambayoyina kamar haka. Wai shin wane irin gibin rauni ne da tattalin arzikin kasar Sin ya samu sakamakon zuwan guguwar annoba da ta rushe rumfunan tattalin arziki na dukkannin kasashen duniya a shekarar 2008 da ta gabata? kuma wadanne irin matakai ne kasar Sin ta dauka wajen farfado da tattalin arzikin kasarta?" To, mun gode, malam Muhammed Idi Gargajiga, da ka aiko mana wannan tambaya. Gaskiyarka, matsalar kudi ta kawo illoli ga tattalin arzikin duniya, ciki har da na kasar Sin, musamman ma ta fannin fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje. Sabo da raguwar bukatun kasashen waje ta sanya dimbin masana'antun Sin da ke fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje sun rage wa ma'aikatansu albashi ko kuma sallamarsu, har ma wasunsu sun lalace. A sa'i daya kuma, wasu kasashe sun dauki matakan kariyar cinikinsu, sabo da haka, sun kayyade har ma sun hana shigar da kayayyaki daga kasar Sin, wanda ya kara tsananta halin da masana'antun kasar Sin ke ciki. Bisa adadin da aka bayar, an ce, yawan cinikin shigi da fici da Sin ta yi da kasashen waje ya ragu cikin watanni hudu a jere. To, a cikin irin wannan hali, tun daga karshen rabin shekarar da ta gabata, gwamnatin Sin ta dauki jerin matakai na tinkarar matsalar, ciki har da kara kudaden jari da gwamnati ke zubawa da inganta karfin jama'a ta fannin sayayya. Sa'an nan, ta tsara shirin farfado da masana'antunta da kuma kyautata tsarin ba da tabbaci ga zaman al'umma. Ban da wannan, Sin ta kuma dauki matakai na bunkasa bukatun gida, tare kuma da tabbatar da karuwar ciniki da kasashen waje." Matakan da Sin ta dauka sun kuma sami yabo daga masanan ilmin tattalin arzikin duniya, Stephen Green, darektan HSBC, yana ganin cewa, matakan da Sin ta dauka na iya tabbatar da imanin jama'a ga kasuwanni, ta yadda za su iya tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar Sin. Ya ce, "Sin na kara taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin duniya, kuma ta iya zama kasa kadai da tattalin arzikinta zai karu da kashi 8% a shekarar 2009, muna farin cikin ganin cewa, a yayin da kasashen duniya ke fama da matsalar imani da amana, tana iya cimma sakamako mai kyau daga matakanta na bunkasa tattalin arzikinta."

To, mun dai amsa tambayar malam Muhammed Idi gargajiga game da tattalin arzikin kasar Sin a gaban matsalar kudi da ke galabaitar da kasashen duniya baki daya, da fatan malam Muhammed Idi Gargajiga ya ji kuma ya gamsu da bayaninmu. Ban da wannan, muna kuma fatan shugabannin G20 za su cimma wata manufa mai kyau a gun taron kolin London, don fid da kasashen duniya daga mawuyacin halin da suke ciki.

Har wa yau, kwanan nan, wasu masu sauraronmu sun fadi albarkacin bakinsu game da taron koli na G20. Ciki har da Samaila Zagga, daga jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya, wanda a cikin sakonsa, ya ce, "wannan taro yana da muhinmancin gaske domin zai tabo matsaloli da kasashe ke fuskanta a fannin kudi da tattalin arziki, ganin yadda duniyan ke cikin wani hali na kaka ni kayi na tattalin arziki da faduwan darajar man fetur, haka kuma matsalar kudi ko tattalin arziki ya yi tasiri a kasashenmu na Afrika da al'ummarta ya sanya yawaitar rashin aikin yi. Ina kyautata fatan taron ya tattauna tare da magance matsalolin kudi a duniya."

Akwai kuma, Faruk Annur, a Sokoto, tarayyar Nijeriya, ya ce, "A gaskiya matsalar dambarwar kudi da duniya ke fuskanta a halin yanzu ya yi tasiri, amma ba mai amfani ba, domin ya kawo wahalhalu ga kasashe da daidaikun al'umma, ya kamata a lura da yadda talakawa ke neman abin sakawa a bakin salati, da-kyar-da-jibin-goshi."

To, muna godiya ga duk wadanda suka aiko mana sakonninsu, kuma da fatan za ku ci gaba da ruwaito mana. (Lubabatu)