Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-24 22:18:59    
Ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet

cri
Masu sauraro, ran 28 ga watan nan da muke ciki rana ce ta tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a jihar Tibet ta kasar Sin, wanda aka yi a ran 28 ga watan Maris na shekarar 1959, kuma tun daga lokacin ne, an fara yin gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet. Amma watakila masu sauraronmu ba ku da wata masaniya a kan wannan tarihi, kuma wasu kafofin yada labarai na kasashen yammaci na kokarin neman gurbata ainihin tarihi, sabo da haka, masu sauraro, a farkon shirinmu na yau, zan dan kawo muku tarihin gyare-gyaren dimokuradiyya da aka yi a Tibet, domin amsa tambayar wasu masu sauraronmu na neman karin bayani game da batun Tibet, ciki har da Faruk Dan Juma, daga Zaria Kaduna, tarayyar Nijeriya, da Hamisu Sani a Kano, Nijeriya da sauransu.

Shekarar 1959 ta alamanta wata muhimmiyar shekara a tarihin jihar Tibet ta kasar Sin. A watan Maris na shekarar, an fara gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet, inda aka yi watsi da tsarin mallakar bayi manoma, kuma daga nan miliyoyin bayi manoma sun sami 'yancinsu.

Kafin shekarar 1959, Tibet ta dade tana karkashin mulkin da ta yi shimkafa da waken addini da siyasa. Bisa takardun tarihi, a tsohuwar Tibet, yawan masu mallakar bayi manoma da suka hada da jami'ai da masarauta da jagoran addini, ba su kai kashi 5% na yawan mutanen Tibet ba, a yayin da yawan bayi manoma ya zarce kashi 90%. Masu mallakar bayi manoma suna mallakar kusan dukannin gonaki da gandunan daji da kuma dabbobi a Tibet, sa'an nan suna iya sayar da bayi manoma ko kuma musanyarsu kamar su abin hannunsu ne. Kana kuma suna iya bautar da su har ma kashe su yadda suka ga dama. A shekarar 1950, daga cikin yawan mutanen Tibet su miliyan 1, akwai dubu 900 da ba su da gidajen kwana.

A shekarar 1951, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta cimma yarjejeniyar 'yantar da Tibet cikin lumana tare da tsohuwar hukumar Tibet, amma bisa hakikanin halin da aka sami Tibet a ciki, ba a yi wa tsarin zaman al'umma na Tibet gyara ba nan da nan. A watan Maris na shekarar 1959, wasu tsirarrun 'yan koma baya mahukuntan Tibet sun ta da bore, don kin yarda da gyare-gyaren da jama'a ke kira da kiyaye tsarin mallakar bayi manoma. Amma bisa goyon bayan dimbin bayi manoma, ba da sauri ba sai aka kwantar da boren, kuma an fara gudanar da gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet yadda ya kamata. Bisa gyare-gyaren da aka yi, bayi manoma sun sami 'yanci da mutunci, kuma sun sami gonaki da kuma kayayyakin aiki. An kawar da tarnaki da dabaibayi da ke kan bayi manoma, kuma sun zama masu gidan Tibet.

Yau ga shi shekaru 50 sun wuce, kuma wata sabuwar Tibet da ke da bunkasar tattalin arziki da hadin kan al'umma da kuma zaman alheri ya bayyana a gaban jama'a. A shekarar 2007, yawan GDP na Tibet ya kai kudin Sin yuan sama da biliyan 34, wanda ya ninka sau 59 bisa na shekarar 1959. Hanyar dogo da ke tsakanin lardin Qinghai da jihar Tibet ta kuma samar da kuzari ga harkar yawon shakatawa a Tibet, har ma yawon shakatawa ya zama wani babban ginshiki ga tattalin arzikin wurin. Sa'an nan, sakamakon kyautatuwar aikin kiwon lafiya da zaman rayuwarsu, matsakaicin shekarun 'yan Tibet a duniya ya kai 67 yanzu, wanda ya karu da shekaru 31 bisa na shekarar 1951.

To, mun dai dan kawo muku tarihin gyare-gyaren dimokuradiyya da aka gudanar a Tibet, da fatan ya taimaka wajen fadakar da ku a kan batun Tibet. Bayan haka, kwanan nan, wasu masu sauraronmu sun aiko mana ra'ayoyinsu dangane da batun Tibet. Mamane Ada daga Yamai, jamhuriyar Nijer, ya ce, "A gaskiya, babu wata babbar matsala da kasar Sin ke fuskanta a game da wannan yanki na Tibet, illa cewa akwai wasu kasashen Turai da na Amurka da ke ma kasar Sin zagon kasa, wato wadannan kasashe na amfani da Dalai lama wajen matsa lamba kasar Sin na cewa, babu 'yancin fada a ji kuma babu dimokuradiyya. Dalai Lama ya zama wani dan amsar shata ne na wadannan kasashe da ba su son ci gaban kasar Sin. Idan aka dauko zancen abin da ya auku a Tibet a 'yan watannin da suka shige, an san cewa, akwai hannun wadannan kasashe a game da kone-konen da aka yi, da kuma rasuwar wasu daga cikin al'ummar wannan yanki da ke son zaman lafiya da kuma ganin ko da yaushe cin hadaddiyar kasa guda cewa da kasar Sin tamkar uwa mai ba da mama. Don haka, ina kira ga hukumomin kasar Sin da su ci gaba da kare wannan yanki nasu daga duk wasu masu neman raba Tibet daga kasar Sin, kuma har kullum Tibet za ta tsaya ga kasar Sin. Baya ga haka, ina fatan ganin magabatan Sin su dauki mataki kan Dalai Lama tun da ba tsohon albarka ba ne, domin duk abin da yake ba na kare addinin Buddah ba ne. Abin da nike fata gare ku ma'aikatan CRI, don Allah ku isar da sakona zuwa ga al'ummar Tibet da kewayanta, kada su yarda su ba da hadin kai ga Dalai Lama, don ba mai kaunar su ba ne, kuma da yardar Allah, Dalai Lama sai ya ji kunya rana tsaka. A halin yanzu, kasashe da yawa na duniya sun gane manufar wannan mutum, don haka tuni suka dawo daga rakiyarsa."

Ga kuma sakon da Salihu Abudullahi Kiyawa, a Federal College of Education,jihar Bichi-Kano,Nijeriya, ya aiko mana, inda ya ce, "A nawa tunanin, a da zarar Tibet ta samu irin abin da take kira "'yanci" ya tabbatar, to, farkon gutsuri-tsoma ke nan, ba sauran zaman lafiya a wannan yanki. Domin wasu kasashe za su samu damar shigowa cikin Tibet din domin yin angizon da zai hana zaman lafiya da ci gaban zamani da tattalin arziki, da yanzu suke wanzuwa a wannan yanki mai albarka.

A yanzu me yankin Tibet ya rasa na abin ya shafi ci gaban zamani, ko kuma akwai hakki da aka hana ta na tafiyar da harkokin more rayuwa ko na bin addininta na 'yan yankinsu? Ni dai a iya sani babu. Saboda haka, Tibet ta yi ta zama a matsayinta na jiha a cikin kasar Sin har abadan abada!"

To, mun gode, malam Mamane Ada da Salihu Abudullahi Kiyawa da aiko mana ra'ayoyinku, kuma muna gaskata cewa, duk wani mai son gaskiya zai amsa kirarku. Muna kuma fatan masu sauraronmu za ku ci gaba da aiko mana ra'ayoyinku game da batun Tibet. (Lubabatu)