Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-23 22:11:50    
Dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin daga kabilar Sala mai bin addinin Musulunci

cri
Yau wato ran 5 ga wata, an bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a nan birnin Beijing, wadda kuma ta kasance kamar hukumar koli ta mulkin kasar Sin, inda a kan tattauna kan burin da kasar Sin take son cimmawa a cikin sabuwar shekara da kudurorin raya kasar, da kuma kada kuri'a a kansu. A gun taron, ana iya samun dimbin musulmai 'yan majalisar da ke bayar da gudummowa sosai wajen samun bunkasuwar kasar. To a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ya zo daga kabilar Sala da ke bin addinin musulunci, wanda ake kiransa Han Yongdong.

Masu sauraro, abin da kuke saurara dazun nan gaisuwa ne da Han Yongdong, shugaban gundumar Xunhua ta kabilar Sala mai cin gashin kai ta lardin Qinghai da ke yammacin kasar Sin ya nuna muku.

Da ya samu labarin kan cewa, za mu watsa wannan bayani ne ga dimbin musulmai na kasashen Afirka, Han Yongdong ya tsai da kuduri kan cewa, ya kamata ya yi wa masu sauraronmu takaitaccen bayani kan tarihin kabilar Sala. Ya ce,'Yan kabilar Sala sun kaura zuwa kasar Sin ne daga kasashen da ke tsakiyar Asiya, ya zuwa yanzu sun riga sun yi zama a kasar Sin har shekaru fiye da 800, kuma yawan 'yan kabilar ya karu daga gomai zuwa dubu 100, a ciki 'yan kabilar dubu 70 suna zaune a gundumar Xunhua, saura kuma suna zama a lardunan Xinjiang da Gansu.

A matsayinta na garin 'yan kabilar Sala, gundumar Xunhua tana kusa da kogin Huanghe, kuma sabo da tana kan filaton Qinghai-Tibet, shi ya sa amfanin gona na wurin na iya samun isasshen ruwa da hasken rana. Domin yin amfani da wannan yanayin rinjaye wajen samun bunkaswa, 'yan kabilar Sala sun sa muhimmanci kan amfanin gona da ke da halin musamman na wurin, wato yaji. Sakamakon yanayin halitta da ke dace da girman yaji, yaji ya samu bunkasuwa sosai a wurin. Sabo da haka kuma manoma 'yan kabilar sun samu alheri. Game da wannan, Han Yongdong ya bayyana cewa,"Lokacin da manoma suka shuka hatsi, yawan kudin riba da suka samu daga gonakin da fadinsu ya kai murabba'in mita 660 ya kai Yuan 400 kawai, amma bayan da suka shuka yaji, wannna jimilla ta kai Yuan fiye da 2000, ta haka yawan kudaden shiga da manoma suka samu ya samu karuwa a bayyane."

Kuma Han Yongdong ya gaya mana cewa, a cikin shekaru 5 ko 6 da suka gabata, sakamakon manufofin da gwamnatin kasar Sin da kuma gwamnatin lardin Qinghai suka bayar wajen samar da taimako a wannan fanni, ba kawai aikin noman yaji ya samu bunkasuwa ba, a'a har ma aikin sarrafa yaji ya samu ingantuwa. Yanzu harkar samar da yaji a gundumar Xunhua ta samu karbuwa sosai a biranen Beijing da Chengdu da kuma jihar Xinjiang, har ma a wasu lokuta, ba su iya biya bukatun kasuwannin wuraren ba. Sabo da haka, Han Yongdong ya gaya mana cewa, a nan gaba, gundumar Xunhua za ta ci gaba da daukar matakai wajen kara raya sana'ar samar da yaji. Ya ce,"Da farko, za mu kafa sansani a cikin gundumarmu wajen raya aikin samar da yaji, daga baya kuma za mu dogara bisa karfin shahararrun masana'antun sarrafa yaji na gundumarmu wajen sa kaimi ga bunkasuwar sansanin, ban da wannan kuma sakamakon ba mu iya samun isassun gonaki wajen shuka yaji a cikin gundumarmu ba, shi ya sa muna cikin shirin shuka yaji a sauran gundumomin da ke makwabtaka da gudumarmu, da kuma wasu wurare na jihar Xinjiang, domin neman habaka wannan sana'a."

Ban da raya amfanin gona bisa yanayin musamman na gundumar Xunhua, Han Yongdong ya bayyana cewa, cikinin waje yana daya daga cikin al'adun gargajiya na kabilar Sala. Wani abin ban sha'awa shi ne, bisa labarin da ya samu, ana iya samun 'yan kabilar Sala fiye da dubu daya a birnin Beijing wadanda suke gudanar da kananan dakunan cin abin fiye da 600. Kuma ya kara da cewa, "A cikin 'yan gundumarmu da yawansu ya kai dubu 120, mutane fiye da dubu 40 su kan fita waje don yin ciniki a ko wace shekara. Shi ya sa ana iya gano cewa, rabin yawan kudaden shiga da manoma suka samu ya zo daga wannan fanni. Ban da yin kasuwanci a biranen Beijing da Shanghai da kuma Hangzhou, mu ma mun aika da manoma masu cin rani zuwa kasashen Masar da Malaysia da Saudi Arabia, ta haka zaman rayuwar manoma 'yan kabilar Sala sun samu kyautatuwa matuka bayan da aka aiwatar da manufar bude kofa a waje da kuma yin kwaskwarima a gida."

Tun da aikin fitar da manoma zuwa waje don gudanar da aikin cin rani ya zama wani muhimmin aikin kara yawan kudaden shiga da manoma ke samu, shi ya sa ko shakka babu, matsalar kudi da ke yaduwa a duk duniya ta kawo illa ga manoma masu cin rani na kabilar Sala. Domin tinkarar matsalar koma gida sakamakon rashin aikin yi, gwamnatin gundumar Xunhua tana daukar matakai a jere. Han Yongdong ya bayyana cewa,"Da farko, mun ci gaba da shirya kwasa-kwasan horaswa don manoma masu cin rani a lokacin hunturu, daga baya kuma muna dukufa kan neman kasuwanni a kasashen da ke shiyyar gabas ta tsakiya, dalilin da ya sa muke yin haka shi ne sabo da ba kawai mu da 'yan kasashen 'yan uwa ne ba, abin mafi muhimmanci shi ne sabo da kayayyakin kasar Sin na iya samun babbar kasuwa a can. Ban da wannan kuma, muna kyautata tsarin samarwa na gundumarmu domin kara raya tattalin arzikinmu na halin musamman, bugu da kari kuma za mu dauki matakin ba da gatanci gare su wajen samar da basusuka don raya ayyukansu. A waje daya kuma mun kara kwarin gwiwar masana'antun gundumarmu da su dauki wadannan manoma."

Idan ana son raya tattalin arzikin wata kabila, to, tabbas ne a sa muhimmanci kan raya aikin koyarwa na kabilar. Han Yongdong ya gaya mana cewa, yanzu 'yan kabilar Sala suna mai da hankali sosai kan shigad da yaransu cikin makarantu, musamman ma bayan da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar soke kudin karatu na makarantun firamare da sakandare na shekaru tara, dukkan yara na kabilar sun samu damar samun ilmi. Shi ya sa Han Yongdong ya ce, yanzu ba zai damu da matsalar shiga makaranta ba, sai dai samun ilmi kafin a shiga makarantar firamare. Kuma ya kara da cewa, "idan an mai da hankali a kan samun ilmi kafin shiga makarantar firamare, to, za a iya warware wasu matsaloli. Na farko shi ne zai iya warware matsalar harshe, in yara su samu ilmi kan harshen Sinanci kafin shiga makarata, to za su iya dace da halin da za su kasance a ciki bayan da su shiga makaranta. Na biyu shi ne sabo da yanzu dimbin 'yan kabilar Sala su kan je cin rani a sauran wurare, shi ya sa ba yadda za a yi sai tsoffin da ke gida su lura da yara, wadanda ba su iya ba da ilmi ga yara, shi ya sa in an mai da hankali a kan aikin samun ilmi kafin shiga makaranta, to za a iya rage damuwar da iyayen yara ke nuna a wannan fanni."

Kafin mu kammala yin hira a wannan karo, Han Yongdong ya gaya mana cewa, shi da 'yan kabilar Sala dukkansu sun nuna maraba da masu sauraronmu da su je gundumar Xunhua, gari na kabilar Sala mai bin addinin musulunci domin ganin kyan ganinsa.(Kande Gao)