Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-22 16:34:17    
Gamayyar kasa da kasa na sa lura kan aikin hadin gwiwar sojojin tekun kasashe daban daban da ake yi a kasar Sin

cri

A ranar 20 ga watan nan, an kaddamar da aikin hadin gwiwar sojojin tekun kasashen daban daban a birnin Qingdao da ke gabashin gabar tekun kasar Sin, kuma an shirya aikin ne don yin murnar cika shekaru 60 da kafa rudunar sojojin teku ta sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin. Wannan karo na farko ne da sojojin tekun kasar Sin ke aiwatar da aikin hadin kai tare da sojojin tekun sauran kasashe. A halin da ake ciki, tawagogin sojojin teku na kasashen 29, da jiragen ruwan yaki 21 na kasashe 14, sun isa tashar jirgin ruwa ta Qingdao, don halartar aikin hadin kai da ake yi a wurin. Sa'an nan gagarumin aikin dake da taken 'neman samun daidaituwa kan teku' ya janyo hankula da yawa daga gamayyar kasa da kasa.

Kasar Amurka ta tura jirgin ruwan yaki na 'USS Fitzgerald' mai dauke da makamai masu linzami zuwa tashar Qingdao don halartar aikin, kana kuma Gary Roughead, wani babban hafsan sojojin tekun kasar Amurka ya jagoranci wata tawaga don kawo ziyara kasar Sin. Wannan ziyarar ta zama ziyarar aikin soja mafi muhimmanci da kasar Amurka ta kawo wa kasar Sin a bana, inda Roughead ya bayyana dangantakar da ke tsakanin sojojin tekun kasashen 2 da cewa tana da yakini, haka kuma ya yi kira ga bangarorin 2 da su 'kara hadin kai, da kuma kawar da bambancin ra'ayi'. Bayan haka kuma, Roughead ya nuna yabo ga kasar Sin da cewa, aikinta na yakar 'yan fashin tekun Somaliya ya ciyar da hadin kan sojojin kasashen 2 gaba sosai.

1 2 3