
Baya ga bikin gargajiya na "Zaotang", a lokacin sallar bazara, 'yan kabilar Lisu su kan shirya giya ta musamman don tarbar baki. Suna waka suna shan giya, domin nuna zafin-nama da zumunta ga baki.
"Ma'anar wakar da muka rera yayin da muke shan giya ita ce, yau mun taru a nan, muna farin-ciki sosai saboda mu abokan arziki ne na juna. Muna yiwa baki tarba."
'Yan kabilar Lisu na kasar Sin su kan nuna zafin-nama ga baki daga wurare daban-daban. Kamar yadda malam Bahaushe ya kan ce, "Gani ya kori ji". Idan kun sami dama, ku zo nan kasar Sin ku kaiwa matsugunar 'yan kabilar Lisu bakunci.
To, masu saurare, mun dai kawo muku wani bayani dangane da yadda 'yan kabilar Lisu suke bukukuwan taya murnar sallar bazara. Yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani za mu dawo domin kawo muku wasu labarai dangane da kananan kabilun kasar Sin. 1 2 3
|