Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-21 15:48:15    
Kallon furanni tare da shan ti a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing

cri

Yanzu lokacin bazara ya yi a nan kasar Sin, inda yawancin halittu ke samun sabon karfi, musamman ma tsire-tsire, wadanda suka sake tohuwa daga karkashin kasa ko kuma suka sake yin zama na kore. Yau bari mu shiga wani lambun zamani na renon tsire-tsire a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin domin kallon kyawawan furanni masu nau'o'i daban daban da kuma shan ti cikin kwanciyar hankali.

Lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing ya fi girma a arewacin kasar Sin a halin yanzu. An gina shi ne a shekarar 1956 tare da renon tsire-tsire masu nau'o'i dubu 10 ko fiye. Bikin kallon furannin wani irin 'ya'yan itaciya masu zaki wato peach da a kan yi a wannan lambun zamani a ko wane lokacin bazara yana matsayin abun da ya fi jawo hankalin dimbin matafiya. A wannan shekarar ma an yi haka. A ran 21 ga watan jiya, an bude irin wannan biki a karo na 21 kuma bikin nuna shahararrun furanni na sassa daban daban na duniya a karo na 6 a lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing, wanda za a rufe shi a ran 5 ga wata. Zhao Shiwei, mataimakin shugaban lambun ya yi karin bayani da cewa, a wannan shekara, za a nuna furanni masu nau'o'i dari 2 ko fiye na misalin tukwane sama da dubu 600. Inda ya ce, ?Bisa sakamakon da muka samu a da, matafiya kusan miliyan 1 da dubu 500 kan halarci wannan biki namu. Furen peach shi ne alamar alheri da wadata da kuma korar shaidan. Shi ya sa mutane suke fatan kallon furannin peach zai iya kawo musu sa'a. Mun dasa itatuwa masu ba da 'ya'yan peach da yawa a lambunmu. Wadannan itatuwa kusan dubu 10 sun hada da nau'o'i 70 ko fiye.

Furannin peach masu ruwan hoda masu haske da ke da kananan kunnuwa sun jawo hankalin dimbin masu daukar hoto. Gu Xiaochen, wani ma'aikacin hukumar birnin Beijing ya je lambun zamani na renon tsire-tsire na Beijing ne tare da masoyiyarsa domin kallon furanni da daukar hoto a karshen mako. Mr. Gu ya gaya mana cewa,?Kallon furannin peach a wannan lambun zamani yana faranta mana rai da ba mu kwanciyar hankali. Sa'an nan kuma, muna son daukar hoto. Furannin peach na da kyan gani irin na musamman, shi ya sa muke neman daukar hoto a irin wannan wuri mai kyan gani.?

1 2 3