Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-08 20:52:23    
'Yan wasan kwallon tebur sabbin jini na kasar Sin sun fara yin fintikau a cikin gasar tace wadanda za su je Yokohama

cri

Za a yi gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur ta duniya ta shekarar 2009 a karshen wannan wata a birnin Yokohama na kasar Japan. Domin tace 'yan wasan da za su iya shiga wannan muhimmiyar gasa cikin adalci, a farkon watan jiya, kungiyoyin wasan kwallon tebur na kasar Sin a bangarorin maza da mata sun shirya gasar musamman ta tace wadanda za su sami damar zuwa birnin Yokohama. Sakamakon gasar ya ba mutane mamaki kwarai da gaske. Dan wasa Ma Lin da ya zama zakara a wasan kwallon tebur a tsakanin namiji da namiji na gasar wasannin Olympic, da kuma Wang Liqin, wanda ya nemi sake samun lambar zinariya a cikin shirin a tsakanin namiji da namiji na gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur ta duniya sun sha kaye, yayin da wasu sabbin jini suka yi musu fintikau.

A shekarun baya, yayin da kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta zabi 'yan wasan da suka shiga gasar fid da gwani ta duniya, ta yi watsi da hanyar da ta taba bi, inda babban malamin horas da wasanni shi ne ke tsai da kuduri kan dukkan wadanda za su sami damar shiga gasar. Yanzu kungiyar kasar Sin ta kan shirya gasar tace wadanda suka dace domin zabo 'yan wasan da za su sami damar shiga gasar. A cikin irin wannan gasa, ga ko wane dan wasa, ya yi suna ne ko a'a, kuma ya dade yana kan matsayin mamban kungiyar kasar Sin ne ko a'a, dukkan wadannan dalilai ba su da amfani ko kadan, sai makin da dan wasa ya samu ne yake amfani gare shi. Gasar tace wadanda suka dace da aka yi a fili cikin adalci ta sami amincewa daga sabbin jini da kuma sauran 'yan wasan kungiyar kasar Sin. A yayin gasar fid da gwani ta duniya da za a yi a birnin Yokohama, 'yan wasa maza 7 da mata 7 na kasar Sin za su shiga ciki. Shi ya sa, a wannan karo, kungiyar kasar Sin ta fito da wannan ka'ida, wato 'yan wasan maza 3 da mata 3 da suke kan gaba a cikin gasar tace wadanda za su je birnin Yokohama za su sami dama kai tsaye, za su je birnin Yokohama domin shiga gasar a tsakanin namiji da namiji da kuma tsakanin mace da mace.

1 2 3