Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-06 22:09:45    
An shimfida hanyoyin mota a kan manyan tuddai??Aikin sufuri a jihar Tibet ya sami kyautatuwa

cri

Bayan da kasar Sin ta soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, gwamnatin kasar ta kara zuba kudade a fannin raya muhimman ababen biyan bukatun jama'a a jihar Tibet, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen daukaka ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar mazauna jihar. Shugaban sashin kula da harkokin zuba jari na kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na jihar Tibet Mista Liu Zhiqiang ya ce: "Daga shekara ta 2001 zuwa 2005, ma'aikatu da kwamitoci daban-daban, da kamfanonin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin sun zuba kudaden da yawansu ya kai Yuan biliyan 51, don raya abubuwan more rayuwar jama'a, da wasu muhimman sana'o'i, wadanda suke zama ginshikai wajen habaka tattalin arzikin jihar."

A ranar 1 ga watan Yuli na shekara ta 2006, an kaddamar da zirga-zirgar hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet, wadda ta kawo karshen tarihin rashin samun hanyar dogo a jihar. A ganin mazauna jihar Tibet, hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet, hanya ce wadda ke iya bunkasa tattalin arziki da samar da zaman alheri ga jama'a. Mataimakin darektan ofishin bada jagoranci ga aikin zirga-zirgar hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet na jihar Tibet Mista Fu Yutao ya nuna cewa: "Kaddamar da hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ya ingiza bunkasuwar jihar, a shekara ta 2007, yawan kudaden da aka samu daga aikin kawo albarka a cikin jihar ya kai Yuan biliyan 34.2, wanda ya karu da kashi 13.8 bisa dari. A halin da ake ciki yanzu, jihar Tibet ta yi ta samun bunkasuwa cikin sauri, haka kuma tsarin tattalin arzikin jihar ya sami kyautatuwa."

A shekara ta 2007, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tsara wani shiri na zuba makudan kudaden da adadinsu ya zarce Yuan biliyan 77 don gina muhimman ayyuka guda 180. Shugaban hukumar kula da harkokin sufuri ta jihar Tibet Mista Zhao Shijun ya bayyana cewa: "Yau da shekaru biyar da suka gabata, yawan kudin da kasar Sin ta zuba a fannin shimfida hanyoyin mota ya kai Yuan biliyan 18.74, zuwa karshen shekara ta 2007, tsawon hanyoyin mota dake shimfide a dukkan jihar Tibet ya kai kilomita dubu 48.6, an kaddamar da zirga-zirgar hanyoyin mota a cikin kashi 90 bisa dari na dukkan garuruwa da kashi 60 bisa dari na dukkan kauyuka a jihar. A halin da ake ciki yanzu, ana gaggauta aikin shimfida hanyoyin mota wanda ba'a taba ganin irinsa ba a cikin tarihin jihar Tibet, ta yadda za'a kawo sauki ga mazauna jihar da adadinsu ya kai miliyan 2.8 a fannin yin zirga-zirga."

Masu saurare, a yanzu haka dai, harkokin sufuri na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin suna bunkasuwa cikin sauri, hakan ba ma kawai ya karfafa cudanya da mu'amala a tsakanin Tibet da sauran lardunan kasar Sin ba, har ma ya habaka tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar mazauna jihar.


1 2