Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-03 15:26:58    
Rukuni na 2 na sojojin tekun kasar Sin suna kan hanyar zuwa tekun Somaliya don aikin ba da kariya ga jiragen ruwa

cri

A ranar 2 ga watan Afrilu da safe, rukuni na 2 na sojojin tekun kasar Sin sun tashi daga tashar Zhanjiang da ke kudancin kasar Sin, za su je tekun Somaliya inda za su maye gurbin rukunin farko don daiwatar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwa na farar hula da suke bin tekun Somaliya da mashigin tekun Aden. Abin na da alamar cewa, aikin ba da kariya na sojojin tekun kasar Sin ya shiga wani sabon mataki, inda zai gudana bisa tsarin karba-karba da kuma mai dorewa.

Abin da muka saurara shi ne babban komandan sojojin tekun kasar Sin ya ba da umarnin tura wadannan jiragen ruwan yaki na rukunin don su kama hanya. Sa'an nan jiragen 2 masu taken Shenzhen da Hauangshan,da suke dauke da makamai masu linzami, sun fara bari tashar don nufa tekun Somaliya,inda sojojin suka tsaya kan shimfidar kasan jirgin ruwa, sun sara wa iyalansu da jama'a da suke yi ban kwana da su a wurin.

Wakilinmu ya tambayi matar wani sojan da ya halarci aikin kan abin da take ji a rai, sa'an nan madam din ta amsa da cewa, tana jin alfahari sosai, kuma tana fatan za su samu zaman lafiya a kan hanya.

Rukuni na 2 na sojojin ruwan kasar Sin masu zuwa tekun Somaliya ya kunshi jiragen ruwan yaki na Shenzhen da Huangshan, wadanda za su hada karfi da wani jirgin daban mai samar da kayayyaki ga jirgin yaki, da sauran jiragen sama masu saukar ungulu, da kuma wasu sojojin kundunbala, inda yawan sojojin rukunin ya kai fiye da 800. Za su maye gurbin sojojin rukunin farko da suka isa tekun Somaliya a watan Disamba na shekarar bara, don ci gaba da ba da kariya ga jiragen ruwan kasar Sin masu bin tekun somaliya, da kuma tsaron jiragen ruwan kasa da kasa masu jigilar kayayyakin agaji.

Wadannan sojojin tekun kasar Sin za su yi tafiya har tsawon mil na teku na 4600, kuma za su ketare mashigin teku na Malakka, da tekun Indiya. Bayan sun isa tekun Somaliya, za su maye gurbin sojojin rukunin farko, bayan da suka gudanar da aikin ba da kariya tare a sau daya a can. Yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa,Yao Zhilou, shugaban rukunin, ya yi alkawarin yin kokari tare da sojojinsa don gudanar da aikin ba da kariya da kyau, ta yadda za a nuna ra'ayin sojojin kasar Sin na neman taka rawa cikin aikin kiyaye kwanciyar hankali a duniya. Yao ya ce,

"Lokacin da muke aiwatar da aikin ba da kariya, kaiwa da komawa ne kawai za mu yi a wajen tekun da muke sintiri, ba za mu tsaya a wata tasha ba, shi ya sa aikin na da wahala. Amma muna ganin wannan aiki a matsayin wata damar da za a yi amfani da ita don horar da sojojin kasarmu, ta yadda za a kara kwarewarsu a fuskar aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya a teku."

A ranar 26 ga watan Disamba na shekarar bara, kasar Sin ta fara tura jiragen ruwan yaki zuwa tekun Somaliya da mashigin teku na Aden don ba da kariya ga jiragen ruwan farar hula, wannan ya kasance karo na farko da sojojin ruwan kasar Sin ke aiwatar da aikin jin kai a kasashen waje. Zuwa yanzu, sojojin ruwan kasar Sin sun ba da kariya ga jiragen ruwan kasar Sin 130, haka kuma sun kare jiragen ruwan kasashen waje wasu 38. (Bello Wang)