Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-02 18:31:23    
Kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa a yayin taron koli na G20

cri

A ran 2 ga wata, an soma taron koli na shugabannin kungiyar kasashe 20, wato G20 a karo na biyu a London, hedkwatar kasar Birtaniya. A yayin taron, shugabanni masu halartar taron za su tattauna muhimman batutuwa iri iri, kamar yadda za a farfado da tattalin arzikin duniya da kara sa ido kan sha'anin kudi da yin gyare-gyare kan hukumomin kudi na duniya da dai makamatansu. Wasu masanan kasar Sin suna ganin cewa, a matsayin wakiliyar manyan kasashe masu tasowa, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa a gun wannan taro.

Mr. Jiang Yuechun, wanda ke nazarin harkokin waje ta fuskar tattalin arziki da tsaron kai a kasar Sin ya ce, "Bisa halin da ake ciki a duk duniya, yanzu kasar Sin ita kadai tana tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arzikinta ba tare da tangarda ba. Bisa sakamakon da kasar Sin da wasu manyan kasashe masu tasowa suka samu a fannin tattalin arziki a cikin shekaru 10 da suka gabata, yanzu matsayinsu a duniya a fannin tattalin arziki yana ta samun karfafuwa. Sabo da haka, a yayin wannan taron G20, za a kara mai da hankali kan amfani da ra'ayoyin kasar Sin, wato kasar Sin za ta iya bayar da karin gudummawa a yayin taron."

Yin kwaskwarima kan tsarin sha'anin kudi na duniya wani muhimmin batu ne na taron koli na sha'anin kudi na London. Game da wannan batu, a bayyane ne kasar Sin ta bayyana ra'ayinta cewa, tana fatan za a iya samun hakikanin ci gaba na yin gyare-gyare kan hukumomin kudi na duniya, musamman ya kamata a kara ikon wakilci da na magana na kasashe masu tasowa a cikin hukumomin kudi na kasa da kasa. Mr. Jiang Yuechun ya ce, matsayin da kasar Sin ke ciki yana bayyana moriyar dukkan kasashe masu tasowa. Mr. Jiang ya ce, "Kasashen yammacin duniya ne suka tsara ka'idojin tabbatar da odar kasuwannin kudi da hanyoyin tafiyar da hukumomin kudi na kasa da kasa. Sakamakon haka, ba a iya bayyana moriyar kasashe masu tasowa kamar yadda ya kamata ba. Sabo da haka, wajibi ne a yi gyare-gyare a kansu. A kan wannan batu, kasar Sin ta bayar da wasu ra'ayoyinta. A ganina, ra'ayoyin kasar Sin suna wakiltar moriyar kasashe masu tasowa."

Game da batun samar da karin kudade ga asusun ba da lamuni na kasa da kasa, wani muhimmin batu daban ne da za a tattauna a yayin taron. Yawan kudaden musaya da ke cikin hannun kasar Sin ya kai dalar Amurka kusan biliyan dubu 2. Sabo da haka, wasu kasashen yammacin duniya suna fatan kasar Sin za ta iya samar da karin kudade ga asusun ba da lamuni na kasa da kasa domin taimakawa kasashen da suke cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki. A fili ne kasar Sin ta nuna goyon baya ga ra'ayin samar da karin kudade ga asusun ba da lamuni na kasa da kasa. Amma a ganinta, ya kamata a samar da kudade ga asusun bisa halin da wata kasa ke ciki yanzu da matsakaicin yawan GDP na kowane mutum na wannan kasa da kuma yadda take dogara da asusun domin tabbatar da ingancin tattalin arzikinta. Bugu da kari kuma, ya kamata a nemi daidaito tsakanin nauyi da iko a lokacin da ake samar da karin kudade ga asusun ba da lamuni na kasa da kasa. Mr. Jiang ya ce, "Ba ma kawai ya kamata a zura ido kan jimillar GDP ta wata kasa ba. Alal misali, yanzu jimillar GDP ta kasar Sin ta riga ta kai matsayi na uku a duniya, amma matsakaicin GDP na kasar Sin ya kai dalar Amurka dubu 3 da wani abu kawai, wato tana baya sosai a cikin duk kasashen duniya. Sabo da haka, ra'ayin neman kasar Sin ta samar da karin kudade ga asusun bai dace da hakikanin halin da kasar ke ciki ba. Bugu da kari kuma, ya kamata a zura ido kan yadda ake rarraba iko a cikin asusun, sabo da yanzu kasar Amurka mai hannu da shuni ce a cikin asusun."

Haka kuma, Mr. Jiang Yuechun ya ce, ko da yake kasar Sin ta soma shiga ayyukan yin gyare-gyare kan odar tattalin arziki da sha'anin kudi ta duniya daga dukkan fannoni, amma ba a iya fadin cewa, yanzu kasar Sin kasa ce mai arziki ba. Har yanzu, kasar Sin kasa ce mai tasowa. Mr. Jiang ya ce, "Dole ne kasar Sin ta tabbatar da daidai matsayinta a duniya, wato kasa ce mai tasowa. Kuma dole ne mu yi harkokinmu kamar yadda ya kamata, kuma ci gaba da raya tattalin arzikinmu." (Sanusi Chen)