Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-01 19:53:57    
Ana jiran samun daidaito tare da kasancewar sabani a gun taron koli na G20 kan sha'anin kudi

cri
Za a kira taron koli a karo na biyu na kungiyar kasashe 20 wato G20 kan sha'anin kudi a gobe wato ran 2 ga wata a birnin London, babban birnin kasar Birtaniya, inda shugabanni daga muhimmai da sabbin kasashe da yankuna na duniya a fannin tattalin arziki za su tattauna kan dabarun tinkarar matsalar kudi. Kuma ana ganin cewa, wannan taron koli taro ne mafi muhimmanci da za a kira a wannan muhimmin lokaci na tabarbarewar tattalin arzikin duniya. Haka kuma manazarta suna ganin cewa, ko da yake da akwai sabani a yayin taron koli kan sha'anin kudi, amma ana sa ran cewa, za a iya samun wasu ra'ayoyi na bai daya.

A yayin taron, shugabanni masu halartar taron za su yi musanyar ra'ayoyi kan inganta aikin daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, da sa kaimi ga farfado da tattalin arziki, da kara sanya ido kan sha'anin kudi na duniya, da tabbatar da kasuwar kudi ta duniya, da kuma yin kwaskwarima kan hukumomin kudi na duniya. Bugu da kari kuma, taron zai tattauna kan yadda za a goyi bayan kasashe masu fama da talauci don haye wahalhalun da suke sha sakamakon matsalar kudi, da kin amincewa da samar da kariyar sha'anin kudi da ciniki, da kuma yin iyakacin kokari don tabbatar da kiyaye muhalli yayin da ake farfado da tattalin arziki.

Ra'ayin bainar jama'a ya nuna hasashen cewa, a yayin wannan taron koli, neman tsara shirin sa kaimi ga tattalin arziki daga manyan fannoni da za a iya samun daidaito a kan shi a duk duniya zai zama wani muhimmin batu da za a tattauna a kai. amma yanzu ana samun kasancewar babban sabani a tsakanin Amurka da kasashen Turai a kan batun. Kasar Amurka tana fatan sauran kasashe za su iya hade kai tare da ita wajen aiwatar da gagarumin shirin sa kaimi ga sha'anin kudi. Amma a yayin taron shugabannin kasashen Turai na lokacin bazara da aka yi a 'yan kwanakin da suka gabata, kasashen Turai sun ci gaba da bayyana ra'ayinsu kan cewa, ba su son samar da karin kudade don sa kaimi ga tattalin arziki. Sabo da haka ana iya gano cewa, a yayin wannan taron koli, Amurka da Turai za su ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu. Amma a waje daya kuma, manazarta sun nuna cewa, watakila bangarorin biyu za su rage sabanin da ke tsakaninsu a yayin taron don neman samun daidaito a fannin moriya domin cimma burinsu na farfado da tattalin arziki.

Amma a idon manazarta, ko da yake akwai sabani a kan shirin sa kaimi ga tattalin arziki, amma tinkarar matsalar kudi abu ne na gagawa a halin yanzu, shi ya sa ake sa ran cewa, za a samu wasu ra'ayoyi na bai daya a yayin taron domin cimma burin inganta farfado da tattalin arzikin duniya.

Da farko, sakamakon kasancewar matsalar samar da kariyar sha'anin kudi da ciniki a wasu kasashe, shugabanni da ke halartar taron za su bayyana ra'ayinsu kan tsayawa tsayin daka na kin amincewa da samar da kariyar zuba jari da ciniki domin sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya cikin sauri, kuma za su yi kira da a kara ciyar da shawarwarin Doha zuwa gaba.

Ban da wannan kuma, game da batun tinkarar matsalar kudi a kasashe masu fama da talauci, ana sa ran cewa, shugabanni masu halartar taron za su yi musu alkawari na samar da taimako gare su don haye wahalhalu. A kwanan nan, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya nanata a cikin wata wasika da ya mika wa shugabannin da ke halartar taron koli, cewar ya kamata a kara samar da taimako ga kasashe masu fama da talauci. Dimbin kiraye-kiraye za su sa kaimi ga samun daidaito a kan batun a yayin taron.(Kande Gao)