Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-01 16:21:20    
Kasashen Afrika na fata za a gabatar da moriyarsu a gun taron koli na kudi na kungiyar kasashe 20

cri
Yanzu kasashen Afrika na fuskantar matsalar raguwar yawan jarin waje, da taimakon kudi daga waje a sakamakon matsalar kudi ta duniya. Yaya za a gabatar da moriyar kasashen Afrika a gun taron koli na kudi na kungiyar kasashe 20 da za a shirya a birnin London? Kuma wane irin bege ne kasashen Afrika suke yi kan wannan taron koli? A cikin shirinmu na yau kuma, za mu kawo muku wani bayani kan wannan.

An mayar da taron koli na kudi na kungiyar kasashe 20 da za a shirya a birnin London a matsayin wani muhimmin dandali da manyan kasashen duniya a fannin tattalin arziki za su yi shawarwari na bangarori da dama, da kuma neman hanyar warware matsalar kudi da ake fuskanta a yanzu. Amma, ana damuwa kan wannan halin da ake ciki na kasar Afrika ta kudu daya kawai daga Afrika za ta halarci taron koli. Ko za a gabatar da moriyar kasashen Afrika sosai a gun taron, ko a'a? Madam Hanna S. Tetteh, ministar kula da harkokin cinikayya da masana'antu na kasar Ghana ta bayyana cewa, ko da yake tana fatan taron koli zai iya kawo moriya ga kasashen Afrika, amma ba ta sa ran alheri kan wannan.

'A lokacin da muke ganin cewa, mun shiga hargitsin kudi, kuma kasashen da ba su da nasaba da tsarin kudi irin na kasashen Turai da Amurka suna ta shan wahala sanadiyyar matsalar kudi, ya kamata mu lura cewa, wannan ba matsalar tattalin arziki ta kasashe masu ci gaba ba, wannan matsala ce da ke kawo tasiri ga dukkan duniya. Idan ba a iya taimaka wa kasashe masu fama da talauci ta fuskar warware matsalar kudi ba, to, duniya za ta kara fama da talauci. Sabo da haka, muna ganin cewa, kara yin la'akari da kasashen Afrika na dacewa da moriyar kasashe masu ci gaba.'

Pat Utomi, shehun malami na kwalejin cinikayya na Lagos shi ma yana ganin cewa, idan kasashe masu ci gaba suna fatan ceton kansu, tilas ne su mai da aikin ceton kasashe mafiya talauci a duniya a matsayin fifiko.

'Kamar yadda shugaban bankin duniya ya ce, tilas ne kungiyar kasashe 20 ta gano cewa, yin amfani da wasu kudade daga cikin shirye-shiryensu na farfado da tattalin arziki don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a kasashe mafiya talauci, wannan na dacewa da moriyarsu.'

Ko shakka babu, zuba jari kai tsaye ga kasashe masu tasowa, wata hanya mai amfani ta fuskar taimake su kan magance matsalar kudi, da raya tattalin arziki. Amma, bisa kididdigar da kungiyar ECOWAS ta bayar an ce, yawan jarin waje da kasashen yammacin Afrika suka samu a bara ya ragu sosai bisa na shekarar 2007. A sa'i daya kuma, watakila kasashe masu ci gaba ba za su iya cika alkawaransu na bayar da taimako ba. Sabo da haka, yanzu kasashen Afrika da yawa sun fahimci muhimmancin yin kokari da kansu, kuma sun dauki matakai don inganta bunkasuwar tattalin arziki a dukkan fannoni. Mataimakin ministan masana'antu da cinikayya na kasar Nijeriya Humphrey Enemakwu Abah ya bayyana cewa,

'Mun riga mun soma raya tattalin arziki na iri daban daban, a hakika dai, wannan muhimmiyar manufa ce ta gwamnatin kasarmu. Yanzu, muna kokarin raya sana'ar kere kere, da kuma kara fitar da kayayyakin sana'o'i, ban da man fetur. Muna fatan bunkasuwar sana'ar kere kere za ta kawo bunkasuwar tattalin arziki a dukkan fannoni.'

Bayan haka kuma, wakilin bankin duniya da ke kasar Nijeriya Onno Ruhl yana ganin cewa, ana bukatar daidaita lokacin da ake gudanar da shirye-shiryen farfado da tattalin arziki na kasashe daban daban, kasar Sin ce za ta iya sauke nauyin.

'Amfanin da kasar Sin ke yi na da muhimmanci sosai. Ina farin ciki da Sin za ta taka muhimmiyar rawa a gun taron koli. Muna fatan kasar Sin za ta hada kai tare da sauran kasashe mambobi, da kuma samu dabarar warware matsala a karshe.'