Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-31 17:20:04    
Kasar Sin za ta ba da gudummawarta bisa karfinta don tinkarar matsalar kudi ta duniya

cri

A ran 2 ga watan Afrilu, za a kaddamar da taron koli na sha'anin kudi a karo na biyu a tsakanin shugabannin kungiyar kasashe 20 a birnin London na kasar Britaniya. Lokacin da matsalar kudi ta duniya ta zama annoba a duk duniya, kuma ake cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki, kasashen duniya sun sa fatan alheri ga wannan taron koli. A kwanan baya, Mr. Gordon Brown, firayin ministan kasar Britaniya ya bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar kasa ce dake halartar tarurukan tattauna batutuwan da abin ya shafa, kuma tana da muhimmanci sosai ga wannan taron koli. Amma, wasu masana sun yi hasashen cewa, a matsayin muhimmin injin da ke raya tattalin arzikin duniya, a kan batun tinkarar matsalar kudi ta duniya, kasar Sin za ta bayar da gudummawarta bisa hakikanin karfinta, kuma za ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin shawo kan wannan matsala tare.

Game da wannan taro, Mr. He Yafei, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya ce, ana sa fatan alheri kan wannan taro a fannoni 5.

"Da farko, ana fatan a yi hangen nesa, kuma a kara yin hadin gwiwa da tabbatar da imanin jama'a domin farfado da kasuwa. Haka kuma, ya kamata a nemi kasashe daban daban da su dauki matakan sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki bisa hakikanin halin da suke ciki, kuma ya kamata a kara daidaita manufofin tattalin arziki daga dukkan fannoni a tsakanin kasa da kasa. A waje daya kuma, ana fatan a sami hakikanin ci gaba wajen yin kwaskwarima kan hukumomin sha'anin kudi na duniya, musamman ya kamata a kara wakilci da ikon magana na sabbin kasuwanni da kasashe masu tasowa. Sabo da haka, dole ne a tsara shirin da ke da hakikanin burin da ake son cimmawa da tabbatar da lokacin da ake neman kammala wannan shiri. Bugu da kari kuma, tabbas ne ana fama da tunanin kariya cinikin waje, kuma ana fatan za a ciyar da shawarwari na zagaye na Doha gaba cikin daidaito daga dukkan fannoni. Daga karshe dai, ana fatan a mai da hankali kan batun neman ci gaba."

Bisa wannan jawabin da Mr. He Yafei ya bayar, za a iya gane cewa, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su iya kara yin hadin gwiwa domin shawo kan matsalar da ake fuskanta tare. Mr. Zhang Shengjun, shehun malamin jami'ar horar da malamai ta Beijing, wanda ke nazarin batutuwan duniya yana ganin cewa, kasar Sin za ta iya bayar da gudummawarta kamar yadda ya dace a gun wannan taro. Mr. Zhang ya ce, "Game da gudummawar da ya kamata kasar Sin ta bayar a gun wannan taro, a ganina, ya kamata dukkan kasashen duniya su daidaita matsayinsu wajen manufofin sa ido kan tattalin arziki daga dukkan fannoni domin shawo kan matsalar kudi ta duniya cikin hadin gwiwa. Ya kamata kasar Sin ta bayar da gudummawarta kamar yadda ya dace."

A kwanan baya, Mr. Zhou Xiaochuan, shugaban babban bankin kasar Sin ya nuna cewa, ya kamata a samar da wani sabon kudin musaya a duniya da ba shi da nasaba da ikon mulkin kowace kasa, kuma za a iya tabbatar da darajarsa. Wannan ra'ayi ya samu amincewa daga kasashen Rasha da Brazil da Mr. Dominique Strauss-Khan, shugaban asusun ba da lamuni na kasa da kasa, wato IMF. Game da ra'ayin Mr. Zhou Xiaochuan, Mr. Han Fuling, wani shehun malamin jami'ar tsakiya ta koyon ilmin kudi ta kasar Sin ya ce, "Lokacin da kasar Sin take samun karfi ta fuskar tattalin arziki, ya kamata ta canja matsayinta na bin ka'idojin wasa kawai, ya kamata ya zama wani mamban da ke halartar ayyukan tsara ka'idojin wasa. Ya kamata kasar Sin wadda kudin musaya da ke cikin hannunta ya kai kusan dalar Amurka biliyan dubu 2 ta bayar da ra'ayoyinsa domin tabbatar da moriyarta da ci gaban tsarin sha'anin kudi na kasa da kasa." (Sanusi Chen)