Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-25 23:18:07    
Sauye-sauyen da mabiya addinin Buddah suka samu a zaman rayuwarsu bayan da aka soke tsarin mulki irin na gwamutsa siyasa da addini

cri

Mabiya addinin Buddah na gargajiyar kabilar Tibet da ke zaune a gidan ibada sun fito ne daga wata kungiyar musamman a jihar Tibet. A shekaru fiye da dubu da suka wuce, mabiya addinin Buddah na zuriyoyi sun sha bamban da zaman al'umma na yau da kullum, kuma sun yada da kuma kiyaye asalin addinin Buddaha a gidajen ibada. Sun taba taka muhimmiyar rawa a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da kuma al'adu, da dai sauransu a jihar Tibet.

'Mabiya addinin Buddah da ke zaune a gidan ibada na Tashilhunpo da ke birnin Shigatse na jihar Tibet suna fara karanta littatafai na addinin Buddaha ne da karfe 5 da rabi na safe, kuma suna yin haka ne tsawon awoyi uku. Gidan ibada na Tashilhunpo wuri ne da Panchan Lama na zuriyoyi ke zaune a ciki tun bayan Panchan Lama na hudu. Tsering Dorje Lama, 'dan shekaru 69, wanda ya shiga gidan ibada na Tashilhunpo a lokacin da shekarunsa na haihuwa suka kai 10. Ya waiwayo cewa, "A lokacin da na shiga wannan gidan ibada, yawan mabiya addinin Buddah da ke zaune a ciki ya kai fiye da 5000. Lallai suna da yawa sosai.'

1 2 3