Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-25 18:42:44    
Sauye-sauyen da mabiya addinin Buddah suka samu a zaman rayuwarsu bayan da aka soke tsarin mulki irin na gwamutsa siyasa da addini

cri


Amma, kafin a yi gyare-gyaren dimokuradiya a jihar Tibet, rayayyun Buddah masu rai, da manyan mabiya addinin Buddah su ne suke kula da harkokin gidan ibada, sauran mabiya addinin Buddaha ba su da iko kan wannan. A shekarar 1959, an kafa kwamitin gudanar da harkokin dimokuradiya a gidan ibada na Tashilhunpo, an zabi mambobin kwamitin ne sakamakon jefa kuri'u da dukkan mabiya addinin Buddah da ke gidan ibadar suka yi. Bayan haka kuma, an tsaida kuduri kan dukkan harkokin gidan ibada bayan da aka tattauna a gun taron da kwamitin ya shirya. A lokacin kuma, an zabi Tsering Dorje shiga kwamitin, don fara ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi, da na gyare-gyare a gidan ibada. Yanzu, ya riga ya zama wani jami'in kwamitin da ke kula da kayayyakin tarihi. Ya gabatar da cewa, 'Yanzu ana gudanar da ayyukan gyare-gyare kan gidan ibada na Tashilhunpo a fannoni guda 12. A waje daya kuma, muna kiyaye kayayyakin tarihi na gidan ibada. Mun soma wadannan ayyuka ne a farkon shekarar da muke ciki.'

Ba kamar Tsering Dorje, da sauran mabiya addinin Buddaha na gargajiya da ke mayar da hankali kan karanta littatafai na addini ba, saurayi Dawa Tsering da ke zaune a gidan ibada na Tashilhunpo yana zamansa na rayuwar zamani. Dawa Tsering, dan shekaru 29 ya gaya mana cewa, ya zabi shiga gidan ibada ne domin bin addininsu.

'Ina son zama a gidan ibada. A lokacin zaman yau da kullum, ina son karanta littattafai na addinin Buddah, a waje daya kuma, ina sha'awar koyon ilmin al'adu, da kamfuta.'

1 2 3