Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-23 23:13:05    
A shekara ta 2008, jimillar kudaden da jihar ta samu a fannin cinikin shigi da fici ya zarce dalar Amurka miliyan 500

cri

Rahoto daga hukumar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya ce, a shekara ta 2008, jimillar kudaden da jihar ta samu a fannin cinikin shigi da fici ya zarce dalar Amurka miliyan 500, wadda ta karu da kusan kashi 30 bisa dari.

Sakamakon munanan tashe-tashen hankula da suka barke a jihar Tibet a ranar 14 ga watan Maris na shekarar bara, gami da rikicin hada-hadar kudi da ya zama ruwan dare a duniya, yawan kudaden da jihar ta samu a fannin cinikin waje ya ragu ainun. Domin shawo kan matsanancin halin da take ciki, jihar Tibet ta rubanya kokarinta wajen kara bude kofa ga kasashen ketare, da bada kwarin-gwiwa ga cinikin shigi da fici, tare kuma da zuba karin kudade domin ceto kasuwanni. Ta haka, a karshen rabin shekarar da ta wuce, cinikin waje na jihar Tibet ya sami farfadowa sosai.

A shekara ta 2008, jimillar kudaden da jihar Tibet ta samu daga aikin samun bunkasa a cikin gida ta kai kudin Sin Yuan biliyan 39.2, wadda ta karu da kashi 10.1 bisa dari idan an kwatanta ta da ta shekara ta 2007. Tattalin arzikin jihar Tibet ya yi ta karuwa da kashi 10 ko fiye bisa dari a cikin jerin shekaru 16 da suka gabata.

A ranar 9 ga wata, a gun taro kan harkokin kasuwanci na Tibet da aka yi a birnin Lhasa, mataimakin shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin Mista Deng Xiaogang ya ce, a shekarar bara, tattalin arziki da zaman al'ummar jihar sun cigaba da samun bunkasuwa, matsakaicin kudin shiga da manoma da makiyaya na jihar suka samu a wannan shekara ya karu da kashi 10 bisa dari ko fiye idan ana kwatanta shi da na shekarar 2007.

A waje daya kuma, bisa labarin da muka samu daga hukumar kula da harkokin kasuwanci ta jihar Tibet, an ce, a shekara ta 2008, jimillar kudin da aka samu daga cinikin shige da fice ta zarce dalar Amurka miliyan 500, wadda ta karu da kusan kashi 30 bisa dari idan an kwatanta ta da ta shekarar 2007, cinikin waje yana kara taka muhimmiyar rawa wajen habaka tattalin arzikin jihar Tibet.