Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-23 23:10:01    
Yadda 'yan kabilar E'lunchun ta kasar Sin ke bikin taya murnar sallar bazara

cri

A halin yanzu, jama'ar wurare daban-daban na kasar Sin, ciki har da 'yan kananan kabilun kasar suna shirya bukukuwa da dama domin taya murnar bikin gargajiya na al'ummar kasar Sin wato bikin sallar bazara na shekara ta 2009. Daidai kamar muhimmancin bikin Kirismetti ga Turawa, bikin sallar bazara ya kasance biki mafi kasaita ga Sinawa a cikin duk shekara. To, a cikin shirinmu na yau, ina so in gabatar muku da wani bayani game da yadda wata karamar kabilar kasar Sin wato kabilar E'lunchun ke bukukuwan taya murnar sallar bazara.

Akasarin 'yan kabilar E'lunchun suna zaune ne a yankin Hulun Bei'er na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da wasu wurare na lardin Heilongjiang dake arewacin kasar Sin, adadin mutanenta ya zarce dubu 10. Ma'anar E'lunchun ita ce, mutane wadanda suke zaune a kan manyan tsaunuka. 'Yan kabilar E'lunchun suna da nasu yare, da kuma wakokin gargajiya domin bayyana farin-cikinsu na jin dadin zaman rayuwa.

A cikin kauyen mafarauta na garin Nanmu E'lunchun dake birnin Zhalantun na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta, akwai wani dan kabilar E'lunchun, wanda ya kasance jagoran mafarauta 'yan kabilar E'lunchun na wurin. Sunan wannan bawan Allah E Fengjun. 'Yan kabilar E'lunchun suna iya waka da rawa sosai. Tsoho E Fengjun ya waiwayi yadda 'yan kabilar E'lunchun wadanda suke zaune a kungurmin daji suke bukukuwan taya murnar sallar bazara a shekaru da dama da suka wuce, inda ya ce:"A zamanin da, yayin bukin sallar bazara, 'yan kabilar E'lunchun suna yin gangami, suna gasa nama, suna zagaya wuta, suna yin rawa da waka akan duk abin da suke so."


Bayan shekara ta 2000, domin kiyaye muhallin halittu, hukumar wurin ta dauki kwararan matakai na haramta farautar dabbobi, haka kuma hukumar wurin ta samar da kudin diyya ga 'yan kabilar E'lunchun wadanda suka ta'allaka zaman rayuwarsu kan farautar dabbobi, da ba su kwarin-gwiwa wajen gudanar da aikin noma, ta yadda 'yan kabilar E'lunchun za su saba da zaman rayuwarsu na sabon salo. Daga iyalin mafarauta zuwa iyalin noma, zaman rayuwar 'yan kabilar E'lunchun ya sami manyan sauye-sauye, inda E Fengjun ya cigaba da cewa:"Da farko, ba mu iya aikin huda ba, shi ya sa muka yi koyi daga wajen tsoffin manoma. A lokacin, a hakika dai ba mu sha'awar aikin noma, muna ganin sauran mutane suna yin aikin ne kawai, amma ba mu yi komai ba. Daga baya, akwai wasu iyalai wadanda suka arzuta ta hanyar gudanar da aikin noma, mafarauta sun soma nasu ayyukan noma. Ta haka, sannu a hankali iyalan mafarauta suka sami wadata, kuma zaman rayuwarsu ya sami gyaruwa kwarai da gaske."

A halin yanzu, kamar iyalin tsoho E Fengjun, 'yan kabilar E'lunchun wadanda suka ajiye bindigoginsu na farautar dabbobi suna jin dadin zaman rayuwarsu na yau da kullum. Ba su rasa abinci ko kayan sutura ba, haka kuma sun gina sabbin gidajen kwana. A lokacin da, 'yan kabilar E'lunchun ba su taba tsammani za su iya zama kamar haka ba. Dan E Fengjun mai suna E Yuming ya ce, yadda 'yan kabilar E'lunchun suke bikin taya murnar sallar bazara a lokacin kuruciyarsa, ya sha bamban sosai idan an kwatanta shi da na yanzu, inda E Yuming ya ce:"A lokacin kuruciyata, sharadin zaman rayuwarmu ba shi da kyau, kuma ba mu shirya bukukuwa da dama ba lokacin da muke bikin taya murnar sallar bazara. A lokacin, babban ginshikin 'yan kabilar E'lunchun shi ne farautar dabbobi a dazuzzuka, shi ya sa muke dafa akasarin abinci da naman daji. Amma a halin yanzu, akwai abinci iri daban-daban a teburin cin abinci, kamar su kayan lambu, da kifi."

Abincin da aka shirya a jajibirin sabuwar shekara na ranar 30 ga watan Disamba da dare bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, abinci ne mafi muhimmanci a duk shekara a cikin zukatan Sinawa. 'Yan kabilar E'lunchun su kan maida hankulansu sosai kan shirya abinci a jajibirin sallar bazara, kowane irin abinci da suka shirya yana da ma'ana ta musamman, domin bayyana fatan alheri ga kowa da kowa. A jajibirin sallar bazara da dare, 'yan kabilar E'lunchun su kan taru suna cin abinci suna jin dadi, suna hira suna tadi, suna rawa suna waka, lallai halin annashuwa ya game ko'ina.
Tsoho E Fengjun ya bayyana dimbin fatan alheri ga kowa da kowa cikin harshensu, inda ya ce:
"Ina fatan kowa da kowa zai samu koshin lafiya da zaman wadata a sabuwar shekara! Barka da sabuwar shekara!"

Mun dai kawo muku wani bayani dangane da yadda 'yan kabilar E'lunchun suke bukukuwan taya murnar sallar bazara. Yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani za mu dawo domin kawo muku wasu labarai dangane da kananan kabilun kasar Sin.